Makarantar Darul Arkam ta Gombe ta yaye mahaddata 78
Makarantar Islamiyya ta Darul Arkam da ke Gombe ta yi bikin yaye dalibanta da suka haddace Alkur’ani Mai girma su 78 a saukarta karo na biyar.Da take jawabi a wurin saukar Kwamishinar ilimi ta Jihar Gombe, Hajiya A’ishatu MB Ahmad, ta ce ma’aikatar za ta ci gaba da taimaka wa makarantun al’umma da kuma malamai […]

Makarantar Islamiyya ta Darul Arkam da ke Gombe ta yi bikin yaye dalibanta da suka haddace Alkur’ani Mai girma su 78 a saukarta karo na biyar.
Da take jawabi a wurin saukar Kwamishinar ilimi ta Jihar Gombe, Hajiya A’ishatu MB Ahmad, ta ce ma’aikatar za ta ci gaba da taimaka wa makarantun al’umma da kuma malamai don ganin an cike gibin da ake samu a fagen ilimi.
Kwamishinar wadda Mataimakin Darakta mai kula da Harkokin Makarantu Alhaji Sadik Muhammad, ya wakilta ta ce wannan makaranta ta Darul Arkam tana cikin makarantun da suka yi fice wajen samar da ilimin addini da na boko a jihar.
A jawabin Babban Limamin Jami’ar Jihar Gombe Dokta Tahir Inuwa Ibrahim ya jawo hankalin mahaddatan cewa su yi kokari su kiyaye ka’idojin Alkur’ani wajen yin aiki da shi kuma ba shi ne karshen neman iliminsu ba.
Babban Daraktan gidan talabijin na Sunnah Tb, Ustaz Ibrahim Adamu Disina, kiran mahaddatan ya yi cewa kada su yi takama da abin da suka samu, yanzu ne suka fara shiga duniyar neman Ilimi.
Ustaz Ibrahim Disina, ya ce tunda yanzu sun samu Alkur’ani yana da kyau su shiga neman ilimin Hadisi saboda Hadisi yakan fassara Alkur’ani kuma sun nemi sauran fannonin ilimin addini.
Babban Bako na Musamman kuma Hakimin Garin Gombe Alhaji Abdulkadir Abubakar, kira ya yi ga iyayen yara su rika biyan kudin makaranta a kan lokaci saboda nagartaccen ilimin da ake ba yaran.
Daga nan sai ya jinjina wa hukumar makarantar Darul Arkam bisa yadda ta tsaya da kafafunta har ta kai matsayin da take a yanzu.
Da yake bayar da takaitaccen tarihin makarantar shugabanta Malam Idris Hamma Adama, ya ce an kafa makarantar ce kimanin shekara 20 da suka gabata, kuma ta fara ne da bangaren matan aure a zauren gidan marigayi Alhaji Aliyu Hassan Sardaunan Pindiga da dalibai tara.
Malam Hamma Adama, ya ce a shekarar 2001 ne makarantar ta fara bangaren boko, inda yanzu daliban sashin suka kai aji hudu na sakandare.
Babban Limamin Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke Gombe Malam Adamu Muhammad Dokoro ne, ya yi wa daliban darasu a harabar makarantar da ke kusa da cibiyar.
A yayin bikin an bude dakin gwaje-gwajen kimiyya da dakin Kwamfuta da na rubuta jarrabawa sai kuma wani gini mai ajujuwan karatu uku da hukumar makarantar ta gina.