Makarantar FAAN ta yaye dalibai 727
Makarantar Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) da ke Kaduna ta yi bikin yaye jami’an kashe gobara a tashoshin jiragen sama da jami’an kula da tsaro a tashoshin da ta horar su 727 a ranar Asabar da ta gabata. Da yake jawabi a wajen taron, Ministan Sufurin Jiragin Sama, Sanata Hadi Sirika ya ce […]
Ministan Sufurin Jiragen Sama Sanata Hadi Sirika lokacin da yake duba faretin da jami’an da aka yaye suka shirya masa.
Makarantar Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN) da ke Kaduna ta yi bikin yaye jami’an kashe gobara a tashoshin jiragen sama da jami’an kula da tsaro a tashoshin da ta horar su 727 a ranar Asabar da ta gabata.
Da yake jawabi a wajen taron, Ministan Sufurin Jiragin Sama, Sanata Hadi Sirika ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da inganta harkokin tsaro a tashoshin jiragen saman Najeriya, ta hanyar bai wa ma’aikatan da suke aiki a tashoshin jiragen saman ingantatcen horo, kamar yadda ka’idojin kungiyar tashoshin jiragen sama ta duniya suka tanada.
Ministan ya yi kira ga ma’aikatan da aka horar su mayar da hankali wajen yin aiki da abubuwan da aka horar da su a tashoshin jiragen saman, don ganin an samu gagarumar nasara.
A jawabinsa a wajen taron, Manajan Daraktan Hukumar, Kyaftin Rabi’u Hamisu Yadudu ya shawarci jami’an da aka yaye su tabbatar suna gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a tashoshin jiragen saman don ganin sun faranta wa matafiya na gida da na waje.
Shi dai wannan biki ya samu halartar Babban Sakataren Riko na Ma’aikatar Kula da Tashoshin Jiragen Saman Najeriya, Injiniya Musa Hassan da sauran manyan jami’an ma’aikatar.
Kuma an mika kyautattukan karramawa ga wadanda suka fi nuna hazaka a cikin jami’an da aka yaye.