Makarantar Firamare mai daliba daya kacal

Harbin babban birnin Heilongjiang da ke kasar Sin, tun daga shekarar 2015 lokacin da aka bude makarantar bayan an sabunta gininta, har zuwa 2017. “Mun gina makarantar ne don inganta koyarwa da samar da kyakkyawna yanayin koyon karatu.” inji shugabar makarantar Tao Fengju, wadda makarantarta take da nisan kilomita 40 daga garin Harbin. An fara […]

Makarantar Firamare mai daliba daya kacal

Harbin babban birnin Heilongjiang da ke kasar Sin, tun daga shekarar 2015 lokacin da aka bude makarantar bayan an sabunta gininta, har zuwa 2017.

“Mun gina makarantar ne don inganta koyarwa da samar da kyakkyawna yanayin koyon karatu.” inji shugabar makarantar Tao Fengju, wadda makarantarta take da nisan kilomita 40 daga garin Harbin. An fara aikin ginin ne tun a shekarar 2014., a cewarta, lokacin da ake ginin dalibai 36 duk an mayar da su makarantar da kekusa da kauyen a Firmaren Taiping.

Duk da haka bayan kammala aikin ginin sai dalibai 35 suka zabi ci gaba da karatunsu a can Taiping.

“Tsawon shekara guda yaran kauyen Liye sun saba da ajujuwa cike da dalibai, kuma iyayensu suna matukar son su ci gaba da haka,” a cewar Yang Shiyan, shugaban makarantar Taiping. “Iyaye sun sanar da  ni cewa suna jin dadin karatun, inda ake da ajujuwa da malamai. Wasu ma iyayen har garin suka koma da zama.”

In ban da Tu kusan kowa ya cimma burinsa

“Kakata ba ta bar ni in zauna a Firamaren Taiping,” inji Tu. “Ta fad amini cewa akwai sababbin abokan karatu da za mu rika wasa tare da zarar an bude makaranta a sabon zangon karatu.”

Mahaifiyar Tu ta rabu da iyalanta lokacin da yarinyar ke da shekara uku, bayan da mahaifinta ya samu tabin hankali. Sai kakanninta suka himmatu wajen rainonta, duk dacewa suna fama da rashin lafiya.

“A zuri’arsu babu wanda zai iya kaita makaranta,” inji Tao. “Kuma yana da hadari ga karamar yarinya ta tafi Taiping ita kadai, duk dacewa kilomita biyu ne nisan.”

Don haka Tu ta koma makarantar kauye, inda ta hadu da Tao da wani malami Liu Wengguo.

“Tana da matsalar koyon karatu,” inji Tao. “Yana da matukar wahala gare ta ta karanta wake, ta yi lissafi. Don haka sai an yi matukar hakuri kafin a samu ta iya tuna wani abu.”

Sannan malamanta ne ke kula da ita tamkar tana gida a kullum. “Tana da harigido, har ta kai ga ta damalmala gashin kanta ta bata tufafinta. Dole sai na gyara mata jikinta ta yi tsaf-tsaf,” inji Tao.

Yarinyar na cin abincin rana tare da malamanta a kullum, saboda babu wanda zai kawo mata abinci.

“Misis Tao ta bukaci in bar mata jikata su rika cin abincin rana tare lokacin da ta fahimci dalibarta ba ta da wani abinci sai burodi a matsayin abincin rana,” a cewar Wang Shurong, tsohuwa mai shekara 64 kakar yarinyar. “Na so in rika biyan kudin abincin amma shugabar makarantar ta ki yarda.”

Tao ta ce: “Ba ma shan wata wahala wajen samar wa yarinya abincin da za ta ci mai dumi.”

A wani lokacin yarinyar kan tafi wani wuri a hanyarta ta zuwa makaranta, kuma kakarta ba za ta iya binta ba. Idan har ba ta isa makaranta kan lokaci ba, sai Tao ta shiga nemanta a kauyen.

Kakar yarinyar kusan kodayaushe takan manta ta daukota (daga makaranta), saboda haka Ai dinguo mai shekatra 52 da ke gadi, shi yake rakata zuwa gida.

“Aiki ne da ya rataya a kanmu mu tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ’yancin samun ilimi,” inji Tao, “Ina da tabbacin cewa kowane malami zai iya yin haka.”

“Muna bai wa Tu irin kayan koyon karatun da ake da su a kowace makaranta,” inji Yang. “ a lokacin sanyi, akwai falale mai fadin sikwaya mita 500 da take amfani da shi wajen wasan sululun kankara a kowane mako, sannan mukan samo malamin Ingilishi da ke koya mata karatu.”

“Malamai na ba mu dimbin taimako, kuma nakan ji an sauke mini nauyi a matsayina na kaka da ke barin jikarta a makaranta,” inji  Wang.

 

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2

’Yan sanda 5 sun rasu a hatsarin mota a Kano

Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu