Makarantar Great Aspirations ta yaye dalibanta karo na farko
Sabuwar makarantar boko mai sunan Great Aspirations da ke unguwar Agege a Legas ta yaye dalibai 23 a karo na farko daga matakin Nursery zuwa Firamare.Da yake yi wa Aminiya karin bayani, jim kadan bayan kammala bikin yaye daliban da aka gudanar a harabar makarantar da ke unguwar Morkaza a yankin Agege, babban daraktan ilimi […]
Sabuwar makarantar boko mai sunan Great Aspirations da ke unguwar Agege a Legas ta yaye dalibai 23 a karo na farko daga matakin Nursery zuwa Firamare.
Da yake yi wa Aminiya karin bayani, jim kadan bayan kammala bikin yaye daliban da aka gudanar a harabar makarantar da ke unguwar Morkaza a yankin Agege, babban daraktan ilimi na makarantar, Malam Mukhtar Shu’aibu Umar ya ce sun samu nasarori masu yawa.
Ya ce, “Gaskiya mun samu nasarori da dama da suka hada da yaye dalibanmu karo na farko, maza 11 da kuma mata 12. Makarantarmu an gina ta bisa ga tsarin da gwamnati ta amince da shi kuma manhajar iliminmu ta dace da kowace manhaja ta ilimi a duniya. Sannan mun bude bangaren koyar da ilimin addinin Musulunci, inda ake koyar da harshen Larabci. Mun fara da yara kadan, amma yanzu muna da yara fiye da 160 tare da ma’aikata 25 da suka hada da direbobi da masu shara da makamantansu.”
Ya ci gaba da cewa, “Babu abin da za mu ce sai dai mu gode wa Allah Madaukakin sarki da Ya yi mana agaji muka kai ga inda muke a yau. Ba za a rasa matsaloli ba, ta bangaren biyan kudin makaranta daga wajen iyayen yara. Kodayake da dama suna biya. Gaskiya dai ba mu da wata matsala da za ta dakile al’amuranmu a yanzu. Mun rokon Allah Ya ci gaba da taimaka mana, har mu cimma burin da muka sa a gaba.”
Ya bayyana cewa burin da suke so su cimma shi ne samar da ilimin da zai inganta al’umma tare da warkar da mutane daga cututtukan jahilci.
“Muna son ganin mun cimma burinmu na gina sashen sakandare, wanda tuni mun sayi fili kuma nan ba da dadewa ba za a fara gini. Muna so mu samar da yara da za su zama abin koyi ga sauran yara tare da ganin cewa makarantarmu ta zama wata cibiya ta yada ilimin boko da na addini a tsakanin al’ummarmu da kasa baki daya.” Inji shi.
Wanda ya gina makarantar, Alhaji Abdulhadi danladi ya yaba wa malaman makarantar kan jajircewar da suke yi wajen ganin dalibansu sun samu ilimi mai inganci tare da tarbiyya tagari.
Ya yi alwashin ci gaba da ba da gudumawarsa wajen ci gaban makarantar ta yadda za ta bunkasa ilimin boko da na addini a tsakanin al’umma.
“Babu abin da ya fi ilimi muhimmanci. Ilimi shi ne ya bambanta dan Adam da sauran halittu. Da ilimi ake samun ci gaba da ingantacciyar rayuwa. Shi ya sa na ga ya dace na gina makaranta da za ta rika baiwa yara ilimin boko da na addinin Musulunci don a samu al’umma tagari.” Inji shi.
Iyaye da dama da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana farin cikinsu da ’ya’yansu suka kammala karatu lafiya.
An gudanar da wasan kwaikwayo a kan muhimmancin ilimi tare da baiwa yara kyaututtuka daban-daban.
daliban da aka yaye sun fito bainar jama’a sun nuna irin kwarewar da suka samu ta hanyar karatu da yin Turanci da Larabci a bainar jama’a don kowa ya shaida ilimin da suka samu.