Makarantar Hadda ta Gidauniyar Sheikh dahiru Bauchi ta yaye dalibai 30

Makarantar Haddar Alkur’ani da Gidauniyar Sheikh dahiru Usman Bauchi ta bude a Minna ta yaye fiye da dalibai 30 da suka haddace Alkur’ani. Bikin walimar saukar da ya gudana a Babban Masallacin Minna ya samu halartar jama’a daga sassan kasar nan. Da yake jawabi a wurin taron, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya kwatanta Alkur’ani Mai […]

Makarantar Hadda ta Gidauniyar Sheikh dahiru Bauchi ta yaye dalibai 30
Makarantar Hadda ta Gidauniyar Sheikh dahiru Bauchi ta yaye dalibai 30

Makarantar Haddar Alkur’ani da Gidauniyar Sheikh dahiru Usman Bauchi ta bude a Minna ta yaye fiye da dalibai 30 da suka haddace Alkur’ani.

Bikin walimar saukar da ya gudana a Babban Masallacin Minna ya samu halartar jama’a daga sassan kasar nan.
Da yake jawabi a wurin taron, Sheikh dahiru Usman Bauchi ya kwatanta Alkur’ani Mai girma da tushen samar da maganin baki dayan matsalolin da suka addabi jama’a musamman a wannan zamanin da mutane ke fama da kuncin rayuwa. Sheikh dahiru Bauchi wanda ya samu wakilcin dansa Sayyadi Muhammad Fatihu dahiru Bauchi ya jinjina wa iyiyen daliban da malaman da suka koyar da daliban, bisa manhajar babbar makarantar da ke Bauchi.
Jarogan Makarantun Malam Umar Muhammad ya shaida wa wakilinmu cewa kimanin shekara bakwai ke nan da Sheikh dahiru Bauchi ya zo Minna ya bude reshen makarantar a Unguwar Fadikpe ta karamar Hukumar Chanchaga, inda kafin a shekara aka samu daliban da suka kusan fin ajujuwan makarantar.
Malam Umar Muhammad ya ce sakamakon kalubalen karuwar dalibai ne ya sa Sheikh dahiru Bauchi ya samar da karin rassa biyu a cikin Minna da wata a Bidda.
Iyayen daliban makarantar da dama sun nuna takaicinsu ganin yadda wasu daga cikin iyayen ke sakaci wurin biyan kudin wata na Naira 400, inda suka ce, akasarin iyayen suna da ’ya’ya a makarantun boko masu zaman kansu inda suke biyan kudin makarantar zango, saboda tsoron kada a koro musu yara.