Makarantar Islamiyya ta koyar da mata 250 sana’o’i a Sakkwato
Makarantar Madarasatul Darasatil Islamiyya Wal-kur’an da ke Unguwar Garge a Sakkwato ta koyar da mata 250 sana’o’in hannu domin dogaro da kansu. Makarantar Islamiyyar tana koyarwa ne a tsarin koyar da ilimin addini da na boko tare da hadawa da sana’a. Kuma ita ce irinta ta farko a Sakkwato, inda ta yaye daliban a ranar […]
Makarantar Madarasatul Darasatil Islamiyya Wal-kur’an da ke Unguwar Garge a Sakkwato ta koyar da mata 250 sana’o’in hannu domin dogaro da kansu.
Makarantar Islamiyyar tana koyarwa ne a tsarin koyar da ilimin addini da na boko tare da hadawa da sana’a. Kuma ita ce irinta ta farko a Sakkwato, inda ta yaye daliban a ranar Lahadin da ta gabata a babban dakin taro na Sakandaren Sarkin Musulmi Abubakar.
A wurin bikin, Shugaban Makarantar Malam Mujitaba Shehu Garge ya ce makasudin sanya koyon sana’a a manjahar karatunsu shi ne don kawar da zaman banza tare da samar da ingantacciyar rayuwa ga mata don tarbiyya ta tabbata, “In aka kawar da jahilci to a samar wa mutane da aikin dogaro da kai shi ne zai taimaki ilimin musamman ga mata. Yanayi ya sauya a yau rashi na sanya shiga matsala, don haka makaranta ta ga dacewar matan da muke koyarwa da zawarawa da ’yan mata bayan mun ba su ilimin sanin addini da zamani, to kuma sai mu karfafi ilimin da sana’a wadda hakan zai sanya ilimin ya yi amfani gare su da al’umma domin uwa ita ce makarantar farko in ta shiga matsala kowa ya shiga,” inji shi.
“Makaranta da kamfanina da Hukumar Kula da Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ne muke hada gwiwa wajen koyar da matan sana’o’in hannu, kamar yin turare da humra da kayan kwalliya da man shafawa da sauransu,” inji Malam Mujitaba.
Ya kara da cewa sun yi tsarin yadda sana’ar za ta dore domin duk wadda suka koya mata sana’a har ta iya, za su rika bibiyarta tare da ba ta jari, kuma in ta hada abin da ta koya, su za su rika saya don sayarwa a kasuwa don kara karfafa mata.
Shugaba ya ce “Wannan bikin shi ne na 9 da muka yi, domin mun fara ne da yaye mata 415, sannan muka yaye 163 yanzu ga shi muna dalibai 250 masu koyon sana’a. Duk idan mun yi wata biyu muna koyar da dalibai ne muke dauka wadansu mu koyar da su sana’a. Kuma idan sun kammala mu ba su takardar shaidar kammala koyon sana’ar, sai kuma mu kulla huldar kasuwanci da wadanda muka koya wa sana’ar. Tana dalibta tana ’yar kasuwa a lokaci daya ta hanyar hada abin da ta koya tana sayarwa.”
Malam Mujitaba ya yi kira ga matan da suka koyi sana’ar su rike sana’o’in da suka koya da muhimmanci, su san ba su da wani mutunci fiye da dogaro da kai kada su yi wasa domin wannan wata dama ce suka samu, “Don haka kada su yi wasa da ita su rike ta don inganta rayuwarsu. Sannan ina tabbatar muku cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen koyar da sana’a. Bayan koyar da matasa fenti da muka yi za mu kara fadada koyar da sana’a ga mata da maza don kawar da rashin aikin yi da jahilci,” inji Malam Mujitaba Garge.