Makarantar Islamiyya ta Nurul-Huda ta tallafa wa marayu a kauyen Giri
Shugabannin Makarantar Islamiyya ta Nurul-Hudda da ke kauyen Giri da ke yankin Gwagwalada a birnin tarayya Abuja sun bayar da zannuwa da yadiddika ga marayu 428 domin yin dinkin karamar Sallah mai zuwa. Shugabar makarantar Hajiya Halima Sa’eed, ta fadi a wajen mika tallafina a ranar Lahadin da ta gabata cewa, makarantar ta yanke shawarar […]
Shugabannin Makarantar Islamiyya ta Nurul-Hudda da ke kauyen Giri da ke yankin Gwagwalada a birnin tarayya Abuja sun bayar da zannuwa da yadiddika ga marayu 428 domin yin dinkin karamar Sallah mai zuwa.
Shugabar makarantar Hajiya Halima Sa’eed, ta fadi a wajen mika tallafina a ranar Lahadin da ta gabata cewa, makarantar ta yanke shawarar bayar da zannuwa da yadiddikan ne don amsa kiran Allah Wanda a cikin Alkur’ani Mai girma Ya ce, duk wanda ya ciyar (ko ya tufatar) da maraya da marasa karfi cikin al’umma sakamakonsa Aljanna ne.
Hajiya Halima Sa’eed ta ce galibin yaran suna cikin kunci saboda yadda iyayensu suke cikin talauci, kuma wannan ne ya sanya makarantar ta yanke shawarar bayar da irin wannan tallafi.
Ta ce akwai wasu daga cikin yaran wadanda suka rasa dukkanin mahaifansu sakamakon hare-haren ta’addanci a Jihar Borno wadanda aka kawo su makarantar ta hanyar dangin.
Ta ce ya zame wa makarantar wajibi ta dauki nauyin irin wadannan yara tunda iyayen wasu daga cikinsu ba su raye, inda ta ce kyale su su rika gararamba a kan titi zai iya jefa rayuwarsu a hadari a kokarinsu na neman abin da za su ci.
Hajiya Halima Sa’eed, wadda har wa yau ita ce shugabar kismud Da’awa wani bangare na makarantar Islamiyyar ta ce tana kuma biyar kudin makaranta ga marayun tun daga ajin firamare na farko zuwa aji shida da kuma wadanda suke ajin farko a karamar sakandare zuwa ajen karshe na babbar sakandare tare da ciyar da su.
Ta ce makarantar tana shirya laccoci ga matan aure a lokacin azumin Ramadan, inda ta ce a wannan lokaci makarantar tana tallagfa wa masu rauni a cikin al’umma.