Makarantar Islamiyya ta shirya bita ga matan aure a Ibadan

Makarantar Markazut-Ta’alimil-Islamiy a karkashin kungiyar Izalatil Badi’ah Wa Ikamatis-Sunnah reshen Sabo Ibadan ta shirya taron kara wa juna sani ga matan aure dari biyu da aka koyar da su ilmin zamantakewar aure da girkin abinci da tsafta. Taron na bana mai taken “Kyakkyawar Zamantakewar Aure, Tushen Samun Al’umma Tagari,” ya samu halartar matan aure daga […]

Makarantar Islamiyya ta shirya bita ga matan aure a Ibadan

Makarantar Markazut-Ta’alimil-Islamiy a karkashin kungiyar Izalatil Badi’ah Wa Ikamatis-Sunnah reshen Sabo Ibadan ta shirya taron kara wa juna sani ga matan aure dari biyu da aka koyar da su ilmin zamantakewar aure da girkin abinci da tsafta.

Taron na bana mai taken “Kyakkyawar Zamantakewar Aure, Tushen Samun Al’umma Tagari,” ya samu halartar matan aure daga unguwannin Sabo da Sasa da Ojoo da Bodija da Zango a birnin Ibadan. Masana a kan harkokin zamantakewar aure a Musulunci ne suka gabatar da kasidu da suka shafi wannan fanni.

Da yake yi wa Aminiya bayani bayan kammala taron na kwana uku, Shugaban kwamitin taron na bana, Ustaz Salisu Lukman Maiborno ya ce: “Asusun makarantar ne ya dauki nauyin shirya wannan taron bita, domin wayar da kan matan aure a kan kyautata zamantakewar aure tsakaninsu da mazajensu da kula da lafiyar kansu da iyalansu

“Haka kuma an koyar da mahalarta taron ilmin girke-girke da muhimmancin tsaftar jiki da muhalli da kula da renon ciki da yin riga-kafin kamuwa da cututtukan da suka fi shafar mata,” inji malamin wanda ya ce taron na bana ya yi daban da na bara musamman ta fannin karuwar

Mahalarta da irin abubuwan da aka koya masu saboda Allah.

daya daga cikin malaman da suka gabatar da kasidu a wajen taron, Malama Halimatu Kabir cewa ta yi, “na gabatar da kasida ne a kan girkin abinci kamar sinasir da miyar ugu da miyar gyada da aka hada da ganyen zogale. Na yi matukar farin ciki da ganin irin yadda mahalarta taron suka kasa kunnuwa suka saurari bayanan da aka yi masu na tsawon wannan lokaci,” inji ta.

Daga bisani shugaban kungiyar Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatus Sunnah na Jihar Oyo, Alhaji Salisu Abdullahi ya jagoranci shugabannin rassan kungiyar da malamai wajen raba takardun shaida ga mahalarta taron tare da walimar cin abinci nau’i daban-daban da mahalarta taron suka girko daga gidajensu domin nuna cewa sun ilimantu da bitar da aka yi masu.