Makarantar Kimiyya International ta yaye dalibanta 70 a Saminaka

Makarantar Kimiyya International da ke Badarawa Hayin Gada Saminaka, a Jihar Kaduna ta yi bikin yaye dalibanta 70 a ranar Asabar da ta gabata. Da yake jawabi a wajen bikin, Mai martaba Sarkin Saminaka, Alhaji Musa Muhammad Sani ya ce maganar ilimi tana da matukar muhimmanci, “Domin yanzu babu abin da yake iya yiwuwa a […]

Makarantar Kimiyya International ta yaye dalibanta 70 a Saminaka
Makarantar Kimiyya International ta yaye dalibanta 70 a Saminaka

Makarantar Kimiyya International da ke Badarawa Hayin Gada Saminaka, a Jihar Kaduna ta yi bikin yaye dalibanta 70 a ranar Asabar da ta gabata.

Da yake jawabi a wajen bikin, Mai martaba Sarkin Saminaka, Alhaji Musa Muhammad Sani ya ce maganar ilimi tana da matukar muhimmanci, “Domin yanzu babu abin da yake iya yiwuwa a duniya, dole sai da ilimin  zamani. Don haka ina kira ga dukan al’ummar wannan yanki su tashi tsaye wajen neman ilimin zamani,” inji shi.

Sarkin, wanda Alhaji Tasi’u Bako Nabawa Saminaka ya wakilta, ya ce bude makarantar Kimiyya International, ba karamin ci gaba ba ne a yankin. Don haka ya yi kira ga iyayen yara da sauran al’ummar yankin, su bai wa makarantar goyon baya da hadin kai.

A jawabin wanda ya gina makarantar, Malam Ibrahim Haruna ya ce suna shirya irin wannan taro ne a kowace shekara don su bai wa iyayen dalibai da sauran mutanen gari dama su ga abin da ’ya’yansu suke yi a makarantar.

Ya ce a bana sun yaye daliban da suka kammala karamar sakandare guda 40 da kuma daliban da suka kammala makarantar firamare guda guda 30. Ya ce daga lokacin da suka bude makarantar a shekarar 2005 zuwa yanzu, sun yaye daliban karamar sakandare 170 da  daliban firamare 200. Kuma a yanzu suna da dalibai sama da 500.

Malam Ibrahim Haruna ya ce babban abin da ya karfafa masa gwiwar bude makarantar, shi ne yadda ya lura yara da dama a yankin ba su iya karatu da rubuta ba. Don haka ya bude makarantar domin ya bai wa yaran yankin dama su samu ginshikin da zai taimaka musu kafin su shiga makarantar sakandare.

Shugaban ya bayana cewa: “Babban burinmu shi ne mu taimaka wa yara, musamman wadanda iyayensu ba su da karfin da za su kai su manyan makarantu masu tsada. Mu samar musu da makaranta a kusa da su kuma mai sauki, wadda za su goge wajen karatu da rubutu, ta yadda za su samu shiga jami’a su karanta duk fannin da suke so ba tare da wata wahala ba. Don haka muna kira ga iyaye su ba mu goyon baya da hadin kai, domin mu ci gaba da samar wa ’ya’yansu ilimi mai inganci.”