Makarantar Kiwon Lafiya ta darikar Tijjaniya ta yaye dalibai 217 a Saminaka

Makarantar Koyon Aikin Kiwon Lafiya ta kungiyar Malaman Makarantun darikar Tijjaniya da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna ta gudanar da bikin yaye dalibai 217 a ranar Lahadin da ta gabata.Da yake jawabi a wajen bikin Mai marbata Sarkin Saminaka Alhaji MusaMuhammad Sani ya ce buba shakka makarantar ta yi kokari wajen koyar da yaran […]

Makarantar Kiwon Lafiya ta darikar Tijjaniya ta yaye dalibai 217 a Saminaka
Makarantar Kiwon Lafiya ta darikar Tijjaniya ta yaye dalibai 217 a Saminaka

Makarantar Koyon Aikin Kiwon Lafiya ta kungiyar Malaman Makarantun darikar Tijjaniya da ke garin Saminaka a Jihar Kaduna ta gudanar da bikin yaye dalibai 217 a ranar Lahadin da ta gabata.
Da yake jawabi a wajen bikin Mai marbata Sarkin Saminaka Alhaji Musa
Muhammad Sani ya ce buba shakka makarantar ta yi kokari wajen koyar da yaran harkokin ilimin kiwon lafiya a yankin.
Ya ce “Da ma wannan aiki na al’ummar Musulmi ne, domin addininmu na
Musulunci ya koyar da mu kiwon lafiya.”
Sarkin wanda Wazirin Saminaka Alhaji Muhammad Rabi’u Umar ya wakilta, ya mika godiya da farin ciki ga wadanda suka bude makarantar, inda ya yi kira ga masu hali da sauran al’ummar yankin su tallafa wa makarantar.
A jawabin shugaban sashin kiwon lafiya na karamar Hukumar Lere, Alhaji Muhammad Sa’adu Kagarko ya yi kira ga masu hannu da shuni kan su rika sanya jari wajen bude makarantun koyon kiwon lafiya, inda ya ce makarantun kiwon lafiya sun yi karanci a kasar nan.
Ya ce kungiyar ta yi abin koyi, don haka ya yi kira ga sauran kungiyoyin addinin Musulunci su yi koyi da kungiyar wajen bude irin wadannan makarantu domin a taimaka wa al’umma.
Ya ce karamar hukumar ta amince da daliban makarantar, kuma za ta yi aiki da su, ta hanyar tura su kananan asibitocinta domin su rika taimaka wa marasa lafiya. Kuma za su mika sunayensu ga kungiyoyin kiwon lafiya na duniya domin su rika yin aiki da su.
A jawabin jagoran makarantun kiwon lafiya na kungiyar Malaman Makarantun Tijjaniyya na Jihar Kaduna, Alhaji Isma’il Sani Isma’il ya ce sun fara shirin koyar da kiwon lafiya a makarantunsu ne a shekara ta 2012.
Ya ce “Mun fito da wannan shiri ne domin mu taimaka wa kanmu da sauran
al’umma baki daya.Kuma mun fara dauko dalibanmu ne daga makarantunmu muka fara koyar da su wannan shiri, don su koma makarantunsu su taimaki ’yan uwansu dalibai da sauran al’umma.”
Ya ce sun samu shawarwari daga babban makarantar kiwon lafiya ta addinin Musulunci (Islamic Medical Foundation) da ke Kaduna, inda suka hada hannu da ita.
Ya ce suna da rassan wannan makaranta aa kananan hukumomin Kaduna ta Arewa da Igabi da Kubau da ta Saminaka a karamar Hukumar Lere.
Ya yi kira ga gwamnati da al’umma su tallafa wa makarantunsu wajen samar musu da wuraren da za su gina mazaunansu na dindindin.
A jawabin shugaban makarantar ta Saminaka Malam Muhammad Auwal Usman Saminaka ya ce sun bude makarantar ce a shekara ta 2013, kuma baya ga dalibai 217 da suka yaye suna da dalibai kusan 300.
Malam Auwal ya ce suna koyar da aikin ungozoma da yadda za a ba da gudunmawa kan kiwon lafiya a cikin al’umma. “Babban burinmu mu samar da jami’in kiwon lafiya a kowane gida a garin Saminaka da kewaye,” inji shi.

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato

Kotu ta soke hukuncin yi wa Jam’iyyar NDC rijista