Makarantar Kiwon Lafiya ta Jega ta dauki dalibai 700

Makarantar Koyon Aikin Kiwon Lafiya ta Jihar Kebbi da ke garin Jega ta dauki dalibai 700 a shekarar karatu ta bana, domin nazari a dukkan darussan da makarantar ke koyarwa.Shugaban makarantar Alhaji Mohammed Atiku Kande ne ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da suka ziyarci makarantar, wadda ta shahara wajen samar da ma’aikatan […]

Makarantar Kiwon Lafiya ta Jega ta dauki dalibai 700
Makarantar Kiwon Lafiya ta Jega ta dauki dalibai 700

Makarantar Koyon Aikin Kiwon Lafiya ta Jihar Kebbi da ke garin Jega ta dauki dalibai 700 a shekarar karatu ta bana, domin nazari a dukkan darussan da makarantar ke koyarwa.
Shugaban makarantar Alhaji Mohammed Atiku Kande ne ya bayyana haka ga manema labarai a lokacin da suka ziyarci makarantar, wadda ta shahara wajen samar da ma’aikatan kiwon lafiya masu kula da aikin kiwon lafiyar al’umma.
Shugaban makarantar ya ci gaba da cewa daliban 700 da suka dauka daga cikinsu akwai ’yan asalin jihohin Sakkwato da Zamfara da Neja da Jihar Katsina.
Alhaji Mohammad Atiku Kande ya tunatar da iyayen yara cewa bayan watanni uku zuwa hudu makarantar za ta shirya wa sababbin daliban jarrabawa duk wanda ya ci shi ne wanda makaranta za ta dauka, sauran wadanda ba su ci jarrabawar ba kuwa za a kore su. Ya ce ya fadi haka ne domin iyayen yara su san da wannan saboda kada su ga ‘ya’yansu sun dawo gida su ga kamar an koro su ne, haka kawai.
Da yake bayyana kadan daga cikin matsalolin da makarantar ke fuskanta, Alhaji Atiku Kande ya yi kira ga gwamnatin jihar ta kara gina musu gidajen malamai da ofisoshinsu da kuma ajujuwan karatun dalibai.