Makarantar koya wa mata sana’o’i ta AWEDI ta yaye dalibanta
Makarantar koyar da matan aure da ’yan mata sana’o’i ta cibiyar bunkasa ilmi da wayar da kan jama’a ta AWEDI da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato, wadda kuma ake kira Markaz ta yaye dalibanta.Da yake jawabi a wajen taron, daraktan makarantar, Alhaji Yahaya Ibrahim Hassan ya bayyana cewa a wannan makaranta suna koya […]
Makarantar koyar da matan aure da ’yan mata sana’o’i ta cibiyar bunkasa ilmi da wayar da kan jama’a ta AWEDI da ke garin Jos, babban birnin Jihar Filato, wadda kuma ake kira Markaz ta yaye dalibanta.
Da yake jawabi a wajen taron, daraktan makarantar, Alhaji Yahaya Ibrahim Hassan ya bayyana cewa a wannan makaranta suna koya wa mata sana’o’in dinkin zannuwan mata da zannuwan gado da saka da girke-girke da man shafawa da man kitso da man wanke mota don tallafa wa matan aure da sauran mata su sami sana’o’in yi.
Ya ce wannan makaranta watanni 6 ake yi, kuma wannan yaye dalibai shi ne kashi na uku. Ya ce a kashi na farko sun yaye dalibai 20; kashi na biyu sun yaye dalibai 15; yanzu kuma kashi na uku sun yaye dalibai 10.
Ya ce wannan makaranta tana daya daga cikin ayyukan AWEDI na ganin an tallafa wa al’umma su sami ayyukan yi, musamman matan aure.
Ya ce, “Muna shirin ganin nan gaba mu bude sashin Asabar da Lahadi domin baiwa mata ma’aikata da ma su ma su koyi sana’o’i”.
Ya yi kira ga al’umma kan su taimaka wa kungiyar AWEDI kan wannan aiki da suka sanya a gaba.