Makarantar koyar da harkokin fim ta yaye dalibai 32 a Kano
Daliban sun sami horo tare da takardar shaida a bangarorin taka rawa a fim daban-daban.
Wata makaranta da ta fara koyar da matasa harkokin fina-finai a Kano, Jammaje Acting Class, a ranar Lahadi ta gudanar da bikin yaye dalibai 32.
Daliban dai sun sami horo ne tare da takardar shaida a bangarorin taka rawa a fim daban-daban domin su zamo jarumai masu tasowa.
A cewar shugaban makarantar, Kabiru Musa Jammaje, an kirkirota ne domin a samar da kwararrun jaruman da za su cike gibin bukatar da ake da ita a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, da ma takwararta ta Nollywood.
Ya ce, “Mun fara tunanin kafata ne a shekarar 2019, lokacin da muka ga cancantar makarantar Jammaje Academy ta bude wannan sashe inda dalibai za su hada fasaharsu da kuma ilimi don a samar da kwararrun jarumai wadanda za su rika taka rawa a fina-finan Hausa da Turanci.
“A sakamakon haka, mun dauki dalibai 40 a karon farko, muka fara lakca a watan Fabrairun 2021, sannan muka kammala a Mayu.
“A watan Yuni, daliban, tare da gudunmawar wasu jaruman Kannywood suka yi wasu gajerun fina-finai guda uku.
“Daliban sun dauki kwasa-kwasai guda uku; ka’idojin taka rawa a fim, wanda Nasiru B. Mohammed ya koyar, da yadda ake taka rawa a fim, wanda Ali Nuhu ya koyar, sai kuma Turanci don jaruman fina-finai wanda na koyar,” inji Kabiru Jammaje.
Shugaban makarantar ya kuma ce ana gudanar da lakca ne a duk ranakun Lahadi, har na tsawon wata uku ba kakkautawa.
Da yake tsokaci yayin bikin, Shugaban Kungiyar Jaruman Fina-finan Hausa reshen Jihar Kano, Alasan Kwalle, ya yaba wa Jammaje saboda kirkiro makarantar, inda ya ce za ta taimaka matuka wajen fito da matasa masu fasaha daga cikinsu.
Taron ya kuma sami halartar fitattun ’yan masana’antar Kannywood kamar su Ali Nuhu da Ado Ahmad Gidan Dabino da Ibrahim Mandawari da Abba El-Mustapha da Bello Ibrahim (Billy-O) da Balarabe Murtala Baharu, da dai sauransu.