Makarantar Koyar da Sana’o’in Hannu ta Dangote za ta dauki dalibai

Cibiyar Koyar da Sana’o’in hannu ta Dangote da ke jihar Kano, ta sanar da azamarta ta daukar dalibai domin horas da su a kan sana’o’in hannu daban daban. Sanarwar da Gwamnatin Kano ta fitar mai dauka da sa hannun Shugaba Kwamitin Tsare-Tsaren Ayyukanta, Rabi’u Sulaiman Bichi, ta ce za a horas da dalibai sana’o’in hannu […]

Makarantar Koyar da Sana’o’in Hannu ta Dangote za ta dauki dalibai

Wani sashe na makarantar

Cibiyar Koyar da Sana’o’in hannu ta Dangote da ke jihar Kano, ta sanar da azamarta ta daukar dalibai domin horas da su a kan sana’o’in hannu daban daban.

Sanarwar da Gwamnatin Kano ta fitar mai dauka da sa hannun Shugaba Kwamitin Tsare-Tsaren Ayyukanta, Rabi’u Sulaiman Bichi, ta ce za a horas da dalibai sana’o’in hannu ashiri a fannoni daban daban.

Makarantar mai suna Aliko Dangote Ultra Modern Skills Acquisition Center, Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ce ta kaddamar da ita a bana.

Ta bude shafinta ga masu sha’awar samun gurbin karatu daga ranar 1 zuwa 8 ga watan Afrilun 2021.

Daga cikin ka’idodin da Cibiyar ta shar’anta, dole ne masu neman gurbin karatunta su mallaki daya daga cikin shaidar kammala karatun digiri, difloma, NCE ko shaidar kammala sakandire a babban mataki ko karami.

Mabukata na iya shiga shafin yanar gizo na makarantar a adireshinta na www.dumsac.org ko kuma kai tsaye a mika takardu a makarantar da ke kan titin Zariya daura da garin Kura.

Daga cikin sana’o’in da makarantar za ta horas da dalibai akwai Kafintanci, Birkilanci, Gyaran Famfo, Gyaran Mota, Gyaran Lantarki, Girki, Gyaran Jiki da Gashi da sauransu.

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano

Ya kamata a kori shugaban INEC —Obasanjo