Makarantar Madinatul Ahbab ta yaye mahaddata 37 a Saminaka

Makarantar Haddar Alkur’ani Mai girma ta Madinatul Ahbab da ke garin Kwaftara kusa da garin Saminaka a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna ta gudanar da walimar yaye dalibanta guda 37 da suka haddace Alkur’ani Mai girma a karshen makon jiya.A jawabin Shugaban Makarantun Madinatul Ahbab na kasa Sheikh Falalu dan’almajiri, ya ce ya […]

Makarantar Madinatul Ahbab ta yaye mahaddata 37 a Saminaka
Makarantar Madinatul Ahbab ta yaye mahaddata 37 a Saminaka

Makarantar Haddar Alkur’ani Mai girma ta Madinatul Ahbab da ke garin Kwaftara kusa da garin Saminaka a karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna ta gudanar da walimar yaye dalibanta guda 37 da suka haddace Alkur’ani Mai girma a karshen makon jiya.
A jawabin Shugaban Makarantun Madinatul Ahbab na kasa Sheikh Falalu dan’almajiri, ya ce ya zama wajibi duk Musulmi ya yi farin ciki da wadannan yara da aka yaye a makarantar.
Ya ce “Akalla muna da irin wadannan makarantu guda 360 a Najeriya da kasashen makwabta, kuma muna tafiya da zamani a makarantun. Muna da daliban da muka tura kasashen Masar da Sudan da Malesiya wadanda suke karatu a jami’o’i daban-daban.”
Sheikh dan’almajiri ya ce: “Babban burinmu shi ne mu bai wa yaran al’ummar Musulmi kyakkyawar tarbiyya domin su zamanto masu amfani ga al’umma baki daya. Don haka
muna kira ga Musulmi su bai wa irin wadannan makarantu goyon baya da hadin kai, saboda irin alherin da suke haifarwa ga jama’a.”
A jawabin Shugaban Makarantar ta Madinatul Ahbab ta Kwaftara Alhaji Adamu Halilu ya ce sun shirya taro ne domin taya dalibansu murnar haddar Alkur’ani Mai girma.
Ya ce, “A bana mun samu wadanda suka haddace Alkur’ani Mai girma da muka yaye su 37. Mun yaye dalibai mahaddata Alkur’ani Mai girma da dama a wannan makaranta kuma wannan ne karo na 25 na yaye daliba a makarantar.”
Ya ce babban burinsu shi ne su ga cewa makarantar ta bunkasa, don haka yanzu suna ci gaba da ginin mazaunin makarantar na dindindin. Ya yi kira ga iyayen yaran makarantar su taimaka wajen biyan kudin makarantar don ta rika sauke nauyin da ke kanta.