Makarantar Majma’ul Birri wal Adab ta yaye dalibai 31
A ranar Asabar da ta gaba ce Makarantar Majma’ul Birri Wal Adab da ke Hayin Malam Bello Rigasa Kaduna ta yaye dalibanta 31. Daga cikin daliban akwai mahaddata Alkur’ani shida, uku mata, uku maza. A cewar shugaban makarantar, Aliyu Aliyu Koromi ya ce bikin saukar shi ne irinsa karo na uku a makarantar. “Daga cikin […]

A ranar Asabar da ta gaba ce Makarantar Majma’ul Birri Wal Adab da ke Hayin Malam Bello Rigasa Kaduna ta yaye dalibanta 31. Daga cikin daliban akwai mahaddata Alkur’ani shida, uku mata, uku maza.
A cewar shugaban makarantar, Aliyu Aliyu Koromi ya ce bikin saukar shi ne irinsa karo na uku a makarantar. “Daga cikin daliban akwai maza 13 mata 12 sannan kuma akwai wadanda suka yi hadda su shida ne maza uku, mata uku. Wannan kuma shi ne sauka na uku da muka yi a wannan makaranta,” inji shi.
Ya kuma kara da cewa hakika makarantar ta yi fice wajen koyar da tarbiyar Musulunci ga dalibanta domin ita ce za ta haska masu rayuwa.
Shi ma a jawabinsa, daya daga cikin manyan shugabannin makarantar, Shaikh Bashir Alsalafi yaba wa malaman makarantar ya yi wajen ilmantar da yaran. Malamin ya kuma yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga iyayen yara da su mayar da hankali wajen ilmantar da ’ya’yansu.
“Babu shakka iyaye na sakaci wajen kula da karatun yaransu, musamman a bangaren ilimin Islamiyya, domin idan ka duba za ka ga abin da ake biya bai taka kara ya karya ba amma wasu iyayen ba su san biya, wanda hakan bai dace ba.
Ya ce ba za ka dora wa gwamnati daukar nauyin makarantun nan ba amma kuma idan suka taimaka wa irin wadannan makarantu zai taimaka wajen rage tabarbarewar tarbiyar yara a cikin kasa.
Shugaban rikon makarantar na biyu, Abdullahi Adamu Atta ýya bayyana cewa kalubalen da suke fuskanta na da yawa. Akwai rashin biyan kudin makaranta da wasu iyaye ba su yi, domin a cewarsa da kudin ake gyaran makaranta tare da biyan kudin malamai. Ya kuma yi kira ga iyayen yara da su rika kawo taimako makarantar ta hanyar ba da shawara da sauransu.