Makarantar Muhammad Inuwa Academy ta yaye dalibai

Makarantar Muhammad Inuwa Academy da ke Ungurawar Rimi a Jos, a Jihar Filato, ta yi bikin yaye dalibai da bayar da kyaututtuka ga daliban da suka fi nuna kwazo.Makarantar ta gudanar da taron ne a dakin taro na Babban Masallacin Jos a ranar Litinin da ta gabata.A jawabin wani malami mai suna Malam Ashiru Sani […]

Makarantar Muhammad Inuwa Academy ta yaye dalibai
Makarantar Muhammad Inuwa Academy ta yaye dalibai

Makarantar Muhammad Inuwa Academy da ke Ungurawar Rimi a Jos, a Jihar Filato, ta yi bikin yaye dalibai da bayar da kyaututtuka ga daliban da suka fi nuna kwazo.
Makarantar ta gudanar da taron ne a dakin taro na Babban Masallacin Jos a ranar Litinin da ta gabata.
A jawabin wani malami mai suna Malam Ashiru Sani Abubakar ya nuna muhimmanci,
musamman a wannan zamani da aka tafi aka bar jama’armu a baya.
Ya ce idan al’umma ta rungumi ilimi za ta samu ci gaba a bangarori daban-daban. Don haka ya yi kira ga al’ummar Musulmi su rungumi harkokin ilimi domin samun ci gaba.
Daraktan Makarantar Alhaji Auwal Muhammad Inuwa wanda Malam Bilya Auwal Muhammad ya wakilta ya cewa an bude makarantar ce don taimaka wa yara wajen ilimintar da su.
Daraktan ya yi kira ga iyayen yara da sauran al’umma su ci gaba da ba makarantar
goyon baya da hadin kai domin ta ci gaba da kudirin da ta a gaba na ilimintar da al’umma.
Tun da farko shugabar makarantar Malama Lami Lawal Abubakar ta ce sun bude makarantar ce shekara hudu da suka gabata. Kuma tana da bangaren raino da firamare
da sakandire, inda ta fara da dalibai 16, amma yanzu tana da dalibai sama da 250.
Ta ce babbar matsalar da suke fuskanta a makarantar ita ce ta rashin biyan kudin makaranta daga wajen iyaye. Don haka ta yi kira ga iyayen yara su kara ba su goyon baya da hadin kai don cimman nasarar ilimintar da ’ya’yansu.