Makarantar musulunci ta horar da limamai da ladanai 2002

Makarantar horar da Alkalai, Limamai da kuma Ladanai, TSJAIM, da ke Jos jihar Filato, karkashin Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a  Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), ta kammala taron bita wa limamai masu jan salla da masu alkalancin gasar karatun Al’qur’ani mai tsarki da masu shugabanci da ma ladanai masu kiran sallah, da yawansu yakai 2002, wadanda makarantar […]

Makarantar musulunci ta horar da limamai da ladanai 2002

Makarantar horar da Alkalai, Limamai da kuma Ladanai, TSJAIM, da ke Jos jihar Filato, karkashin Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a  Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), ta kammala taron bita wa limamai masu jan salla da masu alkalancin gasar karatun Al’qur’ani mai tsarki da masu shugabanci da ma ladanai masu kiran sallah, da yawansu yakai 2002, wadanda makarantar ta kammala horarwa daga shekarar 2001 zuwa 2019.

Shugaban makarantar, Hafiz Aminu Yusuf, shi ya bayyana alkaluman, a wani taron sanin makamar aiki da a ka shirya mu su, a Jos .

Ya ce, an kafa makarantar ne da zummar horar da limamai da ma masu gudanar da harkokin musulunci, waxanda za su sanya al’umma su aiwatar da ibadunsu yadda ya dace da koyarwar addinin musulunci.

Ya kara da cewa, a shekarar nan kawai, makarantar ta dauki dalibai kimanin 233, da suka fito daga jihohi daban daban har da jamhuriyar Nijar.