Makarantar Nurul Huda ta horar da matan aure kan yin sabulu da turare
Rukunin makarantun Nurul Huda bangaren matan aure da ke da rassa a kananan hukumomi uku na Birnin Tarayya, Abuja, ya horar da dalibansa yadda ake yi sabulu da turaren daki a wani mataki na dora su a kan sana’a da za su taimaki iyalansu.Horarwa wadda aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata an zabo […]

Rukunin makarantun Nurul Huda bangaren matan aure da ke da rassa a kananan hukumomi uku na Birnin Tarayya, Abuja, ya horar da dalibansa yadda ake yi sabulu da turaren daki a wani mataki na dora su a kan sana’a da za su taimaki iyalansu.
Horarwa wadda aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata an zabo daliban ne daga rassan makarantun Nurul Huda na kauyukan Gwako da Giri da Kutunku da ke yankin Hukumar Gwagwlada, inda suka hadu ne da takwarorinsu na Dabi da ke yankin Hukumar Kwali da kuma na kauyen Chukuku a yankin Hukumar Kuje, inda aka horar da su a makarantar Giri.
A jawabinta a yayin bikin, shugabar rukunin makarantun, Malama Halima Sa’id, ta ce kasancewar mata ke jagoranci wajen kula da tarbiyyar iyali tun a gida, ya kyautu su rika gudanar da wani abu da zai taimaki iyalin ko da mazajensu ba su nan.
Ta ce iyalai da dama sun samu kansu a cikin halin tsaka mai wuya bayan rasa mazajensu, ko idan mazajen sun rasa aiki.
Shugabar ta yi fata matan za su fa’idantu da abin da suka koya wajen amfani da shi a gida ko sayarwa. Kuma ta ce akwai hukumomin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu daban-daban da ke tallafa wa al’umma a kungiyance, inda ta yi misali da Cibiyar Bunkasa kananan Sana’o’i ta Abuja Enterprise Agency wadda ta tallafa wa rukunin matan aure daga makarantar a baya da rancen kudi mai saukin biya, bayan an koya masu yadda za su yi kiwon kaji da kuma wasu nau’o’in kayan ciye-ciye.
Da take zantawa da kakilinmu bayan taron, Shugabar ta ce sauran ayyukan da makarantun Nurul Huda ke yi sun hada da ayyukan Da’awa, inda wasu daga cikin tsofaffin daliban makarantar ke zama wakilai. Ta ce ayyukan sun hada da ziyartar kauyukan al’ummar Gbagyi don kira da kara fadakarwa a kan Musulunci da gina rijiyoyi da daukar nauyin karatun marayu.
Ta ce daga cikin matsalolin da suke fuskanta akwai yawan kaurar dalibai a yayin da aka sauya wa iyayensu wurin aiki.
Ta ce a baya sun samu tallafi daga Cibiyar Yada Musulunci ta Abuja (Abuja Centre for Islamic Propagation), wajen aikin makaranta da masallaci, sai dai duk da haka suna bukatar karin agaji don karasa wasu makarantunsu biyu a wasu kauyukan Abuja.