Makarantar Nurul Isalam Nasarawa Bacoco ta yaye xalibai
Makarantar Nurul Islam da ke Nasarawa Bacoco, karamar Hukumar Birnin Kalaba ta yaye xalibai matan aure 16 da suka sauke Alkur’ani mai girma. A jawabinsa shugaban kungiyar Limamai da alarammomi na Jihar Kurosriba Manjo Kabiru Yakubu Sa’ad ya kalubalanci mata Musulmi da kuma su waxanda suka sauke Alkur’nin da su sanya tsoron Allah kuma su […]

Makarantar Nurul Islam da ke Nasarawa Bacoco, karamar Hukumar Birnin Kalaba ta yaye xalibai matan aure 16 da suka sauke Alkur’ani mai girma.
A jawabinsa shugaban kungiyar Limamai da alarammomi na Jihar Kurosriba Manjo Kabiru Yakubu Sa’ad ya kalubalanci mata Musulmi da kuma su waxanda suka sauke Alkur’nin da su sanya tsoron Allah kuma su yi aiki da abin da suka karanta a ciki, sannan kuma su rage zafin kishi. Ya ce ba daidai ba ne da zarar mace ta ji mijinta zai kara aure ta xauki makami ta raunata shi, wata ma har da kashewa. “Ina ba ku shawara ku matan nan da muka taru, domin taya ku murnar yayewa da makaranta ta yi maku yau xin nan, da ku yi koyi da darussan da ke cikin Alkur’ani, ku sanya tsoron Allah. Kada mace da ta ji mijnta zai mata kishiya ta xauki makami ta ce za ta halaka shi. A’a, Allah Ya umarci mu maza da mu yi aure daga biyu, uku, huxu ko xaya,” inji shi.
Shi kuwa Mai Unguwar Nasarawa, Alhaji Sani Baba Gombe, kalubalantar iyayen yara ya yi game da kin sanya ’ya’yansu makarantun koyon addini. Ya kuma nuna takaicinsa yadda a nan Kudanci mata suka fi maza. Don haka ya shawarce su da cewa: “Kowane uba ya tabbata ya ba xansa ilmin addini ko ya tura shi zuwa makarantar koyon addini. Rayuwa ba ta yi ga Musulmi da ba shi da ilmin addini,” inji shi.
Barista Musa Abdullahi Maigoro, Mataimakin Gwamnan Kurosriba na musamman kan harkokin baki, ragargazar iyayen yara ya yi na rashin kula da hakkin malamai. “Yau idan ka duba, malamanmu su ne za ka ga mafi koma baya cikinmu. Maimakon mu kyautata masu sai ka ga an samu akasi kana kuma kishiyar addininmu za ka ga malaman addininsu suna fantamawa, suna shiga motocin alfarma amma mu kuma fa wasu ma kyashin su biya kuxin makarantar Islamiyyar ’ya’yansu suke yi; wanda hakan kuwa ba daidai ba ne. To ina kira da babbar murya, mu gyara halayenmu.”
Tun da farko a jawabinsa, babban limamin masallacin Nasarawa Bacoco, Malam Hassan Axxaiyib, jawabin marhabin lale ya yi wa mahalarta bikin yaye xaliban ya yi.
Sarakuna iyayen al’umma, su ma sun tofa albarkacin bakinsu. Alhaji Salisu Abba Lawan Sarkin Hausa-Fulani mazauna Jihar Kurosriba, kira ya yi ga Musulmi su haxa kai, su kuma taimaka wa addinin Allah domin ci gabansa da kuma na Musulmi baki xaya.
Bikin yaye xaliban da aka yi a harabar masallacin Nasarawa Bacoco ya samu halartar manyan limaman jiha da sarakunan gargajiyar jihar ’yan asalin Arewacin Najeriya mazauna jihar da kuma manyan alarammomi da sauran hafizan Alkur’ani.