Makarantar Otaru Islamic Centre ta yaye dalibai 20

Makarantar Otaru Islamic Centre ta Auchi da ke karamar Hukumar Etsako ta yamma a Jihar Edo ta yaye dalibanta su guda ashirin, maza 13 da mata 7, bayan da daliban suka samu nasarar kammala karatunsu a wannan makarantar. daliban sun amshi takardunsu na shaidar kammalawa. A yayin bikin, Otaro na Auchi Halliru Momoh Ekellabe III […]

Makarantar Otaru Islamic Centre ta yaye dalibai 20
Makarantar Otaru Islamic Centre ta yaye dalibai 20

Makarantar Otaru Islamic Centre ta Auchi da ke karamar Hukumar Etsako ta yamma a Jihar Edo ta yaye dalibanta su guda ashirin, maza 13 da mata 7, bayan da daliban suka samu nasarar kammala karatunsu a wannan makarantar. daliban sun amshi takardunsu na shaidar kammalawa.

A yayin bikin, Otaro na Auchi Halliru Momoh Ekellabe III ne ya yi wa wadannan daliban nasiha da cewa su kula kuma su yi aiki da kyakkyawar tarbiyyar da aka koya musu tare kuma da cewa su ci gaba da karatun Alkur’ani a kullum babu fashi, domin ta wannan hanyar ce za ta tabbatar musu da haddar Alkur’anin dauwamamme a kansu.
Bayan haka kuma Otaru ya ce wajibi ne daliban su san cewa Alkur’ani yana koyar da Musulmai hanyar zaman lafiya da hadin kai tare da adalci tsakaninsu da juna da kuma sauran al’umma baki daya. Don haka sai ya yi kira ga malaman addini a kan su koyar da addini kamar yadda ya zo a cikin littafin Allah. “Ina kira ga daukacin limamai da malaman addinin Musulunci da su tashi tsaye su koyar wa mabiyyaansu sakon da ke cikin littafin Allah da hadisan Manzo (SAW).” Kuma sai ya kara da cewa domin Musulunci addini ne na zaman lafiya da hadin kan alumma.
A wajen yaye daliban, shugaban makarantar Malam Umar Fattahi, ya bayyana matukar damuwa game da yadda ya ce yake ganin wasu daga cikin Musulmi ba su damu da neman ilimin Alkur’ani ba. “Ina ganin wasu Musulmin ba su damu da su yi karatun Alkur’ani ba ballantana su nemi sanin ma’anar ayoyinsa da abin da yake karantarwa.”
Ita kuma Gimbiya Salamatu Momoh, daya daga cikin daliban da suka kammala karatun kuma aka yaye su a bana, ta ce ta yi alkawarin za ta yi amfani da abin da ta koya daga cikin Alkur’ani mai girma tare kuma da koyar wa masu bukata.