Makarantar Riyadul kur’an Suleja ta yaye dalibai
Makarantar Riyadul kur’an Mu’assasatul Islamiyya da ke garin Maje Suleja a Jihar Neja ta yaye dalibai 16 da suka kammala karatu inda aka mika masu takardun shaida a karshen makon jiya. Bikin wanda ya samu halartar malamai da shugabannin al’umma na kusa da nesa, ya gudana ne a harabar makarantar da ke Maje a kan […]
Makarantar Riyadul kur’an Mu’assasatul Islamiyya da ke garin Maje Suleja a Jihar Neja ta yaye dalibai 16 da suka kammala karatu inda aka mika masu takardun shaida a karshen makon jiya. Bikin wanda ya samu halartar malamai da shugabannin al’umma na kusa da nesa, ya gudana ne a harabar makarantar da ke Maje a kan titin Abuja zuwa Minna.
A yayin bikin, daliban makarantar sun gabatar da karance-karance daga cikin Alkur’ani da Hadisi tare da fassarasu da Hausa, al’amarin da ya burge mahalarta taron.
Dagacin Dakwa Dokta Alhassan Musa Babachukuri da na Dabara Alhaji Adamu Chidawa da Mataimakin Shugaban karamar Hukumar Suleja Alhaji Salisu Adamu da tsohon shugaban karamar hukumar Malam Rabi’u Barde ne suka mika takardun shaida ga daliban da aka yaye.
A zantawarsa da Aminiya Daraktan Makarantar Malam Ridwan Nasir ya ce makarantar wadda ta fara a shekarar 2000 da bangaren Islamiyyya ta fadada da na boko a shekarar 2002, kuma tana da dalibai kimanin dubu daya a harabobinta uku da ke Suleja da Maje. Ya ce makarantar yanzu haka tana da na renon yara da firamare da sakandare a fannin Musulunci da boko.