Makarantar tsallen kunfu ta Sin ta hada wasan da kwallon kafa

Wata makarantar horar da tsalle-tsallen motsa jiki na kungfu da ke birnin Dengfeng, a dakin ibadar Shaolin da ke tsakiyar kasar Sin, ta shirya koyar da dalibai yadda za su yi amfani da dabarun Kungfu a wajen wasan kwallon kafa.Makarantar na shirin farawa da dalibai maza 50, mata 50, daga cikin daliban kungfu dubu 30 […]

Makarantar tsallen kunfu ta Sin ta hada wasan da kwallon kafa
Makarantar tsallen kunfu ta Sin ta hada wasan da kwallon kafa

Wata makarantar horar da tsalle-tsallen motsa jiki na kungfu da ke birnin Dengfeng, a dakin ibadar Shaolin da ke tsakiyar kasar Sin, ta shirya koyar da dalibai yadda za su yi amfani da dabarun Kungfu a wajen wasan kwallon kafa.
Makarantar na shirin farawa da dalibai maza 50, mata 50, daga cikin daliban kungfu dubu 30 da aka bude musu ajin horo kan wasan kwallo. daliban da aka zava shekarunsu sun farta daga shekaru 10 zuwa 12.
“Gwama dabarun tsalle-tsalle da wasan kwallon kafa, dabara ce ta inganta tsarin wasan kwallon kafa,” a cewar Zhang Wenshen, shugaban sashen wasannin al’adu na karamar hukuma.