Makarantar Ulumul Arabiyya ta cika shekaru 30 da kafuwa

Makarantar Islamiyya da ake kira Ulumul Arabiyya da ke unguwar Agege a Jihar Lagas ta yi bikin cika shekaru 30 da kafuwa tare da karrama wasu fitattun mutane. Hakazalika makarantar ta gudanar da walimar saukar karatun dalibanta karo na 15.Da yake yi wa Aminiya karin bayani kan bikin, shugaban makarantar, kasimu Dauda Usman ya nuna […]

Makarantar Ulumul Arabiyya ta cika shekaru 30 da kafuwa
Makarantar Ulumul Arabiyya ta cika shekaru 30 da kafuwa

Makarantar Islamiyya da ake kira Ulumul Arabiyya da ke unguwar Agege a Jihar Lagas ta yi bikin cika shekaru 30 da kafuwa tare da karrama wasu fitattun mutane. Hakazalika makarantar ta gudanar da walimar saukar karatun dalibanta karo na 15.
Da yake yi wa Aminiya karin bayani kan bikin, shugaban makarantar, kasimu Dauda Usman ya nuna farin cikinsa da Allah Ya ja kwanansa har ya ga lokacin da makarantar ta cika shekara 30. Ya ce dagewa da jajircewa da malaman makarantar suka yi ne ya sa makarantar ta samu nasarori da yawa. Ya yi fatan nan da shekaru masu zuwa makarantar za ta ninka nasarorin da ta samu a baya.
“Ina mika godiyata ga malaman makaranta da kuma tsofaffin dalibanmu saboda goyon bayan da suke ba mu. Ba don hadin kan da muke samu daga wurinsu ba, da ba mu kawo inda muke ba a yau.” Inji shi.
daya daga cikin daliban da suka sauke Alkur’ani, mai suna Musa Sabo Ibrahim Alkantara ya bayyana farin cikinsa da ya sauke Alkur’ani mai girma.
Iyayen daliban da dama da Aminiya ta tattauna da su sun bayyana farin cikinsu da Allah Ya sa ’ya’yansu suka sauke Alkur’ani.
Wadanda makarantar ta karrama sun hada da Sarkin Hausawan Agege, Alhaji Muhammdu Musa Dogon Kadai da Dokta Lawi Shaikh Atiku da Malam Ahmad Tijjani Imam Muktar da Shugaban karamar Hukumar Kontagora ta Jihar Neja, Alhaji Nasiru Muhammad. Sauran sun hada da Alhaji Muhammad Lawal S. Malami da babban limamin Agege da Hajiya Zainab Talatu Falke da Alhaji Gambo Data da kungiyar Kanzul Ahbab da kungiyar Abna’ul Faida da Malam Ayuba Imam da Alhaji Shehu Yaro da Alhaji Kabiru Rufa’i da Alhaji Safyanu Lawan da sauransu.
daliban makarantar sun gudanar da karatun Alkur’ani mai girma. Makarantar Ulumul Arabiyya ta cika shekaru 30 da kafuwa.