Makarantar Umar Bn Khattab Suleja ta yaye dalibanta karo na 6
A ranar Lahadin da ta gabata ce Makarantar Umar bn Khattab da ke Titin Dan Sakkwato a Unguwar Kaduna Road da ke yankin Suleja a Jihar Neja ta yi bikin yaye dalibanta karo na shida. Bikin yayen daliban wanda ya gudana a farfajiyar makarantar firamare ta unguwar, an yaye dalibai 15 maza da mata da suka […]
Xaliban da suka yi sauka
A ranar Lahadin da ta gabata ce Makarantar Umar bn Khattab da ke Titin Dan Sakkwato a Unguwar Kaduna Road da ke yankin Suleja a Jihar Neja ta yi bikin yaye dalibanta karo na shida.
Bikin yayen daliban wanda ya gudana a farfajiyar makarantar firamare ta unguwar, an yaye dalibai 15 maza da mata da suka sauke Alkur’ani Mai girma, da kuma dalibi daya Alaramma Usman Gambo Lawal da ya haddace Alkur’ani Mai girma.
Da yake gabatar da wa’azi a wajen bikin, Sheikh Ahmad Sambo, ya bayyana matukar farin cikinsa da kokarin da makarantar ke yi wajen koyar da dalibai ilimi da tarbiyya, sai ya yi bayani a kan muhimmanci ilimi da tarbiyya, inda ya tabo batun rikicin haihuwa da sauransu. “Idan mace ta haihu a wata shida, haihuwar ta yi domin Allah Ya ce haihuwa da shayarwa wata 30 ne, sannan a wani wajen Allah Ya ce cikakkiyar shayarwa wata 30. Ke nan idan ka cire shekara biyu cikin wata 30, za ka samu wata shida,” inji shi.
A jawabin Dagacin Bakin Iku Malam Musa Shu’aibu ya jinjina wa kokarin makarantar da shugabanta, Malam Umar Gambo bisa kokarin da suke yi wajen koyar da daliban makarantar, sannan ya ja hankalin mutanen garin su dage wajen tarbiyyantar da ’ya’yansu ilimin addini da na zamani, inda ya ce babu wanda zai yi alfahari da da barawo da wanda ba ya jin magana.
Daliban makaranta da masu saukar sun nuna bajintarsu da kwarewarsu a karatun Alkur’ani da sauran darussa a filin saukar.
Daga cikin abubuwan da aka gudanar a wajen bikin, akwai tantancewa da tabbatar da haddar Alkur’ani na Alaramma Usman Gambo Lawal wanda shi ne alaramma tilo da ya haddace Kur’ani a bana. Da ya fito fili Alaramma Tameem ya ja masa Kur’ani ya karanta a gaban masu kallo domin tabbatar da haddar da ya yi.
Haka kuma an gabatar da wasan kwaikwayo kan alkali mai gaskiya da ba ya karbar rashawa a cikin harshen Larabci da Ingilishi.
Malamai da ’yan siyasa da masu rike da sarautun gargajiya da makarantu da dalibai da sauran ’yan uwa da abokan arziki ne suka halarci saukar.
Makarantar Umar bn Khattab ta fara karatu ne da dalibai 10, amma yanzu tana da dalibai 500 da suka hada da bangaren Islamiyya, da na hadda da bangaren matan aure da na boko.