Makarantar Zaid Bn Thabit ta Ajingi ta yaye dalibai 27
A ranar Lahadin da ta gabata ne Makarantar Zaid Bn Thabit Litahfizul kur’an Waddarasatul Islamiyya da ke Ajingi a Jihar Kano ta yi bikin saukar karatun dalibanta karo na hudu. Da yake jawabi a wajen bikin saukar karatun shugaban makarantar Malam Ahmad Abdullahi, kira ya yi ga Musulmi musu hannu da shuni su taimaka wa […]
A ranar Lahadin da ta gabata ne Makarantar Zaid Bn Thabit Litahfizul kur’an Waddarasatul Islamiyya da ke Ajingi a Jihar Kano ta yi bikin saukar karatun dalibanta karo na hudu.
Da yake jawabi a wajen bikin saukar karatun shugaban makarantar Malam Ahmad Abdullahi, kira ya yi ga Musulmi musu hannu da shuni su taimaka wa makarantar don shawo kan matsalolin da take fama da su.
Malam Ahmad Abdullahi, ya ce an bude makarantar ce a ranar 10 ga Jimada Ula, shekarar 1426 Bayan Hijira wadda ta zo daidai da ranar 17 ga Yulin shekara ta 2005, tare da dalibai 22 maza da mata da ajin karatu daya amma a yanzu tana da dalibai 659 da ajujuwa tara.
Ya ce ganin yadda cikin ’yan shekaru makarantar ta bunkasa tana da matsaloli don haka suke rokon karamar Hukumar Ajingi da masu hannu da shuni su shigo don ba da tasu
gudunmawar wajen samar musu da karin ajujuwan da ofishin shugaban makaranta da na malamai da ban-daki da ruwan sha.
Shugaban kungiyar iyaye da malamai (PTA) kuma babban limamin Ajingi Alhaji Abdullahi Bello, ya roki iyayen yara su rika biyan kudin makarantar domin da su ake aiwatar da wasu ’yan aikace-aikacenta.
Alhaji Abdullahi Bello, ya nemi karamar hukumar ta shigo ciki don bada gudumawarta na ganin ana gudanar da ayyukan makarantar cikin sauki.
dalibai 27 ne suka sauke Alkur’ani Mai girma, 16 maza, 11 mata kuma taron ya gudana ne a harabar makarantar da ke Unguwar Nasarawa bayan Asibitin Ajingi.