Makarantu 79 na da malami 1 kowannensu a Bauchi

Malami daya ke koyar da daukacin dalibai duk darussa a makarantun

Makarantu 79 na da malami 1 kowannensu a Bauchi

Wata makaranta da aka rufe saboda hare-haren ‘yan bindiga

Akalla makarantu 79 ne ke da malami daya kowannensu a Ƙaramar Hukumar Misau ta Jihar Bauchi.

Hukumar Ilimin Bai-daya A Matakin Farko (SUBEB) ta jihar ta nuna cewa malamai daya-daya da makarantun ke da su ne ke koyar da dalibai duk darussa, saboda karancin malamai a makarantun firamaren jihar.

Daraktan kula da makarantu a hukumar, Karijo Umar, ya ce “A Ƙaramar Hukumar Misau kadai makarantu akalla 79 ne ke da malamai daya kowannensu. Duk da cewa babu makarantar da ba ta da malami a jihar.

“A hakan ma gara ƙananan hukumomin Misau da Alƙaleri a kan wasu, sai mutum ya je zai gane wa kansa irin halin da makarantun suke ciki,” in ji Karijo, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya kara da cewa, “A garin Bauchi akwai makarantun da a aji guda za a samu dalibai 250, kuma Malami daya ke koyar da su.”

Karijo Umar ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyin ’yan jarida a wurin taron da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya shirya domin haɓaka shigar ƙananan yara makarantu a ƙananan hukumomin Misau da Alƙaleri na jihar.

A kan haka ne ya ce hukumarsa ta fara tura malamai daga makarantun da ke da malamai da yawa domin rage giɓin da ake da shi a makarantun masu ƙarancinsu.

Ya bayyana cewa hukumar SUBEB ba ta da ikon daukar malamai, sai dai idan an dauke su ta tura su wuraren da za su yi aiki.

Hukumar kula da malamai ta jihar ce ke da alhakin daukar su, shi ya sa SUBEB ke ba ta shawarar abin da ya kamata.