Makarantu biyu sun yaye mahaddata 45 a Kano

Makarantar Madrasatu Sheikh Salisu Litahfizul kur’ an Wattajwid da ke Unguwar Sharada Kano, ta yaye dalibai maza da mata 25 da suka haddace Alkur’ ani Mai girma, yayin da takwararta Madrasatu Hubbun Nabiyyi Tudun kadiriyya, Sharada ta yaye mahaddata 20. Shugaban Makarantar Madrasatu Sheikh Salisu ,Ustaz Miftahu Salisu ya ce sun yaye mahaddata 25 ne […]

Makarantu biyu sun yaye mahaddata 45 a Kano
Makarantu biyu sun yaye mahaddata 45 a Kano

Makarantar Madrasatu Sheikh Salisu Litahfizul kur’ an Wattajwid da ke Unguwar Sharada Kano, ta yaye dalibai maza da mata 25 da suka haddace Alkur’ ani Mai girma, yayin da takwararta Madrasatu Hubbun Nabiyyi Tudun kadiriyya, Sharada ta yaye mahaddata 20. Shugaban Makarantar Madrasatu Sheikh Salisu ,Ustaz Miftahu Salisu ya ce sun yaye mahaddata 25 ne a yayin bikin yaye daliban a harabar makarantar. Ya ce makarantar ta fara ne da dalibai 13 kacal, amma a yanzu haka tana da dalibai 60. “Baya ga koyar da karatun Alkur’ ani Mai tsarki, muna koyar da sauran darussan ibada da hadisi da tarihi da sauransu. Ya yi kira ga iyaye su kara himma wajen ba ’ya’yansu ilimi, musamman na addini domin su san yadda za su bauta wa Allah.  Ustaz Miftahu ya ce har yanzu makarantar ba ta da muhalli na kanta, sai dai sun taya wani fili da aka ce za a sayar musu Naira miliyan uku da rabi.  A jawabin Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim, ya nanata muhimmancin ba yara ilimi tun suna kanana tare da bayyana ilimin Alkur’ ani da babban haske ga Musulmi a duniya da Lahira. Ya yi kira ga gwamnatoci su hada karfi da al’umma wajen habaka ilimin addini da na zamani. A makarantar Madrasatu Hubbun Nabiyyi, shugabanta Ustaz Hussaini Muhammad Auwal, ya ce sun yaye mahaddata maza da mata 20. Ustaz Auwal ya ce baya ga haka daliban sun sauke wasu littattafai hudu da suka hada da Umdatul-Ahkam da Hayatul Islam da Ishmawi da kuma Iziyya.