‘Makarantun Islamiyya ne tushen gyara tarbiyyar matasa’

Shugaban Matasa na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen karamar Hukumar Jos a Jihar Filato kuma shugaban makarantun Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da ta Abdullahi bin Mas’ud da ke Gangaren Jos, Malam Kabiru Muhammad Chidawa ya ce makarantun Islamiyya ne tushen gyara tarbiyyar matasa a kasar nan. Malam Kabiru Muhammad Chidawa ya bayyana […]

‘Makarantun Islamiyya ne tushen gyara tarbiyyar matasa’
‘Makarantun Islamiyya ne tushen gyara tarbiyyar matasa’

Shugaban Matasa na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen karamar Hukumar Jos a Jihar Filato kuma shugaban makarantun Sheikh Ja’afar Mahmud Adam da ta Abdullahi bin Mas’ud da ke Gangaren Jos, Malam Kabiru Muhammad Chidawa ya ce makarantun Islamiyya ne tushen gyara tarbiyyar matasa a kasar nan. Malam Kabiru Muhammad Chidawa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Jos, inda ya ce duk yaron da ya yi karatun addini, tun yana karami Allah zai sanya masa tausayi a zuciya, kuma zai san darajar iyayensa tare da guje wa shaye-shayen miyagun kwayoyi da guje wa shiga kungiyoyin daba.

Ya ce, ya kamata gwamnati ta kula da makarantun addini na Musulunci da na Kirista ta hanyar gina wa irin makarantun ajujuwa tare da biyan albashin malaman da suke koyarwa a cikinsu. Su kuma masu hannu da shuni su rika gina makarantu suna daukar malamai suna biyansu albashi.
Ya ce babbar matsalar da suke fuskanta a makarantun, ita ce mutane ba sa daukar makarantun da daraja wajen biyan kudin makaranta na ‘ya’yansu. Don haka ya yi
kira ga iyayen daliban makarantun su rika ba makarantun goyon baya da hadin kai.