Makarantun Madinatul Ahbab da Madrasatu Sheikh Salisu Litahfizul kur’an sun yaye dalibai
Makarantar Madinatul Ahbab Wat Talamizil kur’an da ke Kano ta gudanar da bikin saukar Alkur’ani Mai girma karo na 53 a harabar makarantar da ke Unguwar Fagge.A jawabin shugaban makarantar, Khalifa Sheikh dayyib Sheikh Haruna Rasheed, ya ce a tsawon kimanin shekara 40 da kafawa, makarantar ta yada rassanta a Najeriya da wasu kasashen makwabta, […]

Makarantar Madinatul Ahbab Wat Talamizil kur’an da ke Kano ta gudanar da bikin saukar Alkur’ani Mai girma karo na 53 a harabar makarantar da ke Unguwar Fagge.
A jawabin shugaban makarantar, Khalifa Sheikh dayyib Sheikh Haruna Rasheed, ya ce a tsawon kimanin shekara 40 da kafawa, makarantar ta yada rassanta a Najeriya da wasu kasashen makwabta, inda a yanzu haka take da rassa 336 a kusan dukkan jihohin Arewa da kuma Legas da kasashen Nijar da Kamaru da Chadi.
Ya yi kira ga gwamnatoci da kuma al’umma su rubanya kokari wajen tallafa wa irin wadannan makarantu.
Daraktan makarantar na Jihar Katsina, Malam Abdullahi Lawan ya ce babban taimakon da suke bukata shi ne masu kudi da gwamnati su taimaka su gina musu fulotan da suke da su don samar musu da ajujuwan karatu.
Manyan bakin da suka halarci taron sun hada da tsohon Jakadan Najeriya a Saudiyya, Farfesa Ahmad Sa’idu Galadanchi da Sheikh Nazir Ahmad Daura da wakilin Gwamnan Jihar da wakilin shugaban Jami’ar Azhar ta kasar Masar, Sheikh Usamaddin Najjar da ’yan rakiyarsa, Sheikh Samirush Shahid da Sayyid Mahmoud Abdulkadir.
Ita kuwa Madrasatu Sheikh Salisu Litahfizul kur’an Wat Tajwid da ke Unguwar Sharadda ta yaye dalibai maza da mata 25 ne da suka haddace Alkur’ani Mai girma.
Shugaban makarantar Ustaz Fatihu Salisu Sharadda ya ce makarantar wadda ta faro da dalibai 13 yanzu haka tana da dalibai 60. Ya ce baya ga koyar da karatun Alkur’ani suna koyar da wasu littattafan ibada da Hadisi da tarihi da sauransu.
Ustaz Miftahu ya ce har yanzu makarantar ba ta da muhallin kanta, sai dai sun taya wani fili da aka ce za a sayar musu Naira miliyan uku da rabi.
A jawabin Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim, ya nanata muhimmancin ba yara ilimi ne tun suna kanana, inda ya ce ilimin Alkur’ani babban haske ne ga Musulmi duniya da lahira. daya daga cikin iyayen makarantar, Alhaji Shehu Uba Gabari, ya yi kira ga masu kudi da kungiyoyin taimakon al’umma su ba da gudunmawa don samar wa makarantar mazauni na dindindin.