Makarantun ’yan gudun hijira na neman dauki a Borno
Tun daga lokacin da hukumomi a Jihar Borno suka bayyana bude sansanonin ’yan gudun hijira a wasu wurare da nufin samar da matsuguni ga mutanen da rikicin Boko Haram ya rutsa da su, wadansu daga cikin masu ruwa-da-tsaki a harkar ilimi suka yi kokarin ganin ana koyar da yara karatun boko a sansanonin. A yayin […]
Wani sashe na wata makarantar sansanin gudun hijira a Maiduguri
Tun daga lokacin da hukumomi a Jihar Borno suka bayyana bude sansanonin ’yan gudun hijira a wasu wurare da nufin samar da matsuguni ga mutanen da rikicin Boko Haram ya rutsa da su, wadansu daga cikin masu ruwa-da-tsaki a harkar ilimi suka yi kokarin ganin ana koyar da yara karatun boko a sansanonin.
A yayin yunkurin an samu hadin kan iyaye da wadansu malaman sa-kai wajen koyar da yaran ilimin boko a matakin farko. Su ma kungiyoyin sa-kai sun taka rawa wajen agaza wa ilimin yaran a sansanonin ’yan gudun hijirar, wajen samar da littattafai da jakunkuna da sauran kayayyakin karatu.
Haka ma Gwamnatin Jihar Borno a karkashin jagorancin Alhaji Kashim Shettima, ta yi iya nata kokarin wajen tallafa wa ilimin yaran ta fuskoki da dama, sai dai kuma an ce idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai, domin har yanzu akwai wasu makarantu a sansanonin ’yan gudun hijirar da ke bukatar tallafin gwamnati don ci gaba da samun ingantaccen ilimi. Duk da cewa akasarin ’yan gudun hijirar sun koma garuruwansu, har yanzu akwai wadansu da ba su iya komawa ba saboda wasu dalilai.
Iyaye da malamai sun roki Gwamnatin Jihar Borno ta waiwayi makarantun da suke sansanonin ’yan gudun hijira don gyara su, saboda wadansu dalibai a gindin itace suke daukar darasi a yayin da wadansu kuma ke dauka a tsakiyar rana, kasancewar akwai wasu ajujuwan da ba a rufe su ba.
Malam Bukar Kachallah, daya daga cikin iyayen yaran wanda ya fito daga Karamar Hukumar Marte, ya bayyana wa Aminiya cewa, “A gaskiya muna tausaya wa yaranmu da ba su wuce shekara 10 ba da suke daukar karatu a tsakar rana. Ya kamata a tausaya wa yaran a ba su kariya daga zafin ranar da kuma kamuwa da cututtuka. Ganin gwamnati da masu ruwa-da-tsaki a harkar ilimi sun nanata mana muhimmancin ilimi ga rayuwar dan Adam ne muka kawo yaranmu, to amma ba dadi a ce mun zo mun same su a irin wannan yanayi. wajibi ne gwamnati ta taimaka wajen inganta iliminsu ta yadda za a ci gaba da ba mu kwarin gwiwar tura su makaranta.”
Malam Ibrahim Sani, wani daga cikin malaman makarantar sansanin gudun hijira na NYSC da ke Unguwar Moduganari Tashar Kano a Maiduguri, ya ce “A gaskiya muna samun cikas a harkar koyarwarmu a irin wadannan wurare na ’yan gudun hijira saboda rashin isassun kayayyakin aiki da ajujuwa. Daliban makarantar firamare a akasarin sansanonin suna koyon karatu ne cikin wahala, don a wasu wuraren za ka ga aji ne amma ba rufin kwano a wasu wuraren a gindin bishiya ake karatu, yayin da a wasu wuraren kuwa a filin Allah ake koyar da su, komai ruwa komai rana.” Gwamnan Jihar, Alhaji Kashim Shettima ya sha nanata cewa “Wannan gwamnatin namu tana kokarin inganta harkar ilimi ta kowace fuska don haka ne ma muka kafa dokar ta-baci a harkar ilimi a jihar don yaki da wancan mummunan dabi’ar Boko Haram da ta haramta ilimin boko da na addini, don haka muke sake fasalin tsarin makarantun ta hanyar gudanar da sababbin gine-gine ko gyare-gyare da kuma samar da kayayyakin aiki a makarantun.”