Makarin Matsananciyar Sha’awa 2
Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da zasu zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayanin hanyoyin da matasa za su bi don magance matsalar matsananciyar sha’awa. Dafatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar […]
Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da zasu zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayanin hanyoyin da matasa za su bi don magance matsalar matsananciyar sha’awa. Dafatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar dasu, amin.
Lakanin karya dafin matsananciyar sha’awa
Hanya ta 7 da matashi zai bi don dakushe kaifin matsananciyar sha’awa: Yana da matukar alfanu ga matashi mai fama da matsananciyar sha’awa ya kasance koda yaushe akwai wani al’amari da ya sa a gabanshi ya ke aiwatarwa, ya tarkato aikin da bai son yi ko wanda yake ganin ya fi karfinsa ya yi ta yi, in kwakwalwarsa ta kasance koda yaushe akwai abinda ke gabanta, a hankali za ta kone kuzarin shaukinta har ya kasance babu kuzarin jin motsuwar sha’awa kuma. Matashi ya kiyayi zama haka nan ba ya yin komai, domin a irin wannan lokacin ne shedan kan lallabo ya tsirar da tunanin sha’awa cikin zuciya, in ko matashi na aiwatar da wani aiki kusan koda yaushe, to ko shedan ya tsirar masa da tunanin sha’awa, to wannan tunanin ba zai yi tasiri ba. Ko kallo ne matashi zai yi, to ya fi masa alheri ya kalli abubuwan karuwar ilimi, ba fina-finan labaran soyayya ba, ko na kide-kide da wake-wake, domin wadannan duk wasu abubuwan ne ma su hassasa ruruwar wutar sha’awa cikin jiki.
Hanya ta 8: Yawan karfi da tsanantuwar sha’awa na iya zama alheri mara iyaka ga mai fama da su in dai ya gano dabarar da zai sarrafa su su haifar da alheri ga rayuwarsa maimakon su yi ta motsowa kodayaushe ba bisa ka’ida ba. Kamar yadda na taba fada a wannan fili, sha’awa ba komai ce illa daya daga cikin shau’ukan dan’adam, kuma duk wani shauki na dan’adam na bukatar kuzari lokacin motsawarsa cikin jiki da zuciya. Sha’awa ta kasance ta fi kowane kuzari karfi a dalilin tana amfani da duka kalar kuzari ukun nan na jikin dan’adam, watau kuzarin aikin karfi, kuzarin ma’aikatar hankali, da kuzarin shau’uka a duk lokacin motsuwarta. Binciken masana kimiyya ya tabbatar dukkannin manyan mutane da suka shahara suka yi suna a duniya ta wani fanni, irin su manyan masana kimiyya, kirkira, masana hikimomi, manyan masu mulki, Allah SWT Ya wadatu su da yawan karfin sha’awa da yawan tsanantuwarta, amma sai basu biye ma son zuciyarsu sun konar da wannan dimbin kuzarin a banza ba wajen dulmiya cikin tunane-tunanen alfasha da neman mata, sai dai suka runka karkatar da wannan dimbin kuzarin sha’awarsu wajen aiwatar da muhimman abubuwa wadanda suka kawo ci gaba a rayuwar dan’adam a dalilin haka su kuma suka yi suna duniya ta sansu, ya kasance ana ambaton su har bayan ransu. Don haka matashi ko magidanci mai tsananin sha’awa ya kamata ya tashi ya mike kuma ya dage, ya juyar da wannan dimbin zinariyar sha’awar da Allah SWT ya azurta shi da ita zuwa ga wani abin da zai zama abin alfaharin gareshi da duk wani nashi. Mu yi dubi zuwa ga manyan mutanen da suka yi suna da karfin su ba da karfin wasu ba, ko karfin zalunci, inda sun biye ma sha’awar su da son zuciyarsu, lallai da basu kai ga wannan matsayi ba. Ba kuzarin da ya kai kuzarin sha’awa karfi, don haka in ya yi yawa ko in ba a bukatar shi wajen ibadar aure, ana iya juyar da shi a cimma wani tsayayyen buri na rayuwa, maimakon a yi barnarsa wajen bin mata ko a yi asararsa haka nan a banza. Da fatan Allah Ya bada ikon dagewa, amin.
Duk lokacin da sha’awa ta motso ma mai fama da matsananciyar sha’awa, to ya san yadda zai yi ya karkatar da tunanin shi daga wannan sha’awar zuwa wani abin daban. Misali, duk lokacin da igiyar tunanin sha’awa ta bijirowa matashi, sai ya yi sauri ya tsinke ta, ta hanyar saka wani tunanin daban cikin zuciyarsa wanda bai da nasaba da sha’awa, misali, sai mutum ya yi ma kansa wani abun da zai sa dole ma’aikatar hankalin sa ta sakki wancan tunanin ta koma ga abin da ke faruwa a jikin sa a wannan lokacin, misali, mutum na iya sanya robali (rubber band) a hannunsa, sai ya ja shi da karfi ta yadda zata tsalle shi ya ji zafi sosai, ko ya ciji hannunsa, ko dan yatsan sa cizo mai zafi a duk lokacin da irin tunanin nan ya bijiro masa, dole kwakwalwa nan take ta yanke ta bar wancan tunani ta koma ga na jin zafi, domin kwakwalwar dai guda daya ce, zai yi wuya ta saurari abubuwa biyu masu karfi a lokaci daya!
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a koda yaushe, amin.