Makarkashiyar durkusar da Arewa
Tun bayan kaddamar da juyin mulkin Jamhuriya ta farko a 1966. Ta bayyana a fili karara game da makirci da kutungwilar da aka shirya domin ruguza arewa a lokaci guda. Arewa ta yi rashin manyan ‘yayanta tun daga kan farar hula, “yan siyasa ga zuwa sojoji masu damara. Kamar su firayim minista na farko kuma […]
Tun bayan kaddamar da juyin mulkin Jamhuriya ta farko a 1966. Ta bayyana a fili karara game da makirci da kutungwilar da aka shirya domin ruguza arewa a lokaci guda. Arewa ta yi rashin manyan ‘yayanta tun daga kan farar hula, “yan siyasa ga zuwa sojoji masu damara. Kamar su firayim minista na farko kuma na karshe, Abubakar Tafawa balewa, Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello. A bangaren sojoji an yi rashin su Birgediya Zakari Maimalari, Laftanar Kanar Largema, Kanar Kur Muhammed, Kanar Pam da sauransu, wadanda ba za su lissafu ba a wannan fili.
Wadanda suka aikata wannan danyen aikin ba su yi nadama ba, ba rantana su bayar da hakuri. A’a an ji suna cewa sun kashe majici, amma ba a sare kan ba. Domin idan har akwai sauran ‘yan Arewa a cikin gwamnati za su basu wahala kenan. An shirya kashe sarakunanmu, don haka aka kiraye su Ibadan akan shugaban kasa Ironsi, zai masu jawabi kuma suka taru duka. A wata hira da jaridar Rariya tayi da Laftanar Janar Jerimiah Useni mai ritaya ta ranar 27 ga Satumba, 2013. “Ya bayyana cewa kafin taruwar sarakunanmu a Ibadan an shirya wa Ofisoshi fati, an sayi kayan shaye-shaye, an kawo mana a wurin. Wato tun da na shiga aikin soja, ban taba ganin inda aka sayi kayan shaye-shaye, masu yawan gaske kamar ranar ba. Ashe wai shiryawa aka yi idan mun yi ta shan ruwa mun bugu, sai a zo a bude mana wuta. To haka aka shirya a mana a bataliya ta hudu ta Ibadan, don a lokacin mu ake jin tsoro. Saboda an san mu ne aka kashewa, Birged Kwamanda Largema”. Wannan mummunan kuduri bai samu nasara ba, ta hanyar hambarar ta Ironsi da aka yi.
Na yi wannan takaitaccen bayanin na sama ne a matsayin shinfida, don a fahimci makarkashiyar da aka dade ana shirya wa Arewa, don ganin bayan ta. Bayan ballewar yakin basasa wanda Ojukwu ya haddasa, sojojin Arewa sun nuna kishin kasa, ta hanyar sadaukaar da rayuwarsu da yi da gaske don ganin Najeriya ba ta wargaje ba. Kusan duk ‘yan Arewa ne suka jagoranci rundunonin kwato yankin Biafara, musamman kwamandojin runduna ta daya, da ta biyu, watau Janar Murtala Muhammed da kuma Janar Mamman Shuwa.
A lokacin da Najeriya za ta koma bisa tafarkin mulkin dimokuradiyya a 1999. An hana duk wani dan Arewa neman tsayawa takarar shugabancin kasar nan a kowace jam’iyya, inda Olu Falaye ya yi takara a jam’iyyar A.P.P yayin da Obasanjo shi kuma ya yi wa jam’iyar P.D.P takara, wadda ta samu nasara, wadanda dukkan su ‘yan Kudu ne. A zamanin mulkin Obasanjo an zarge shi da nuna kabilanci a wurin rabon mukamai tsakanin Kudu da Arewa. A wasu lokutan an samu ballewar rikice-rikice a wasu sassan kasar nan da ke da nasaba da addini da kabilanci, inda aka yi ta kashe ‘yan Arewa da kone dukiyar su, kamar a Lagos, Shagamu, da kuma Onisha. Amma gwamnatin tarayya ta kasa daukar matakin kawo karshen zubar da jinin akan lokaci, tare da biyan diyya ga wadanda suka rasa rayukansu ko dukiyarsu. Gwamnatinsa ta shude yayin da Arewa ba ta tsinci wani abin kirki ba da suna romon dimokuradiyya, sai dai duk lalacewar gwamnatinsa, ba a taba samun tashin bom ba da sunana kai hari.
A tarihin Najeriya kaf, yankin Arewa bai taba samun kansa cikin halin kaka-ni-ka-yi ba da tagayyara kamar zamanin shugaba mai ci a yanzu, Ebele Jonathan. Bayan hawansa kan mulki abu na farko da ya fara ba mu a matsayin somin tabi shi ne dakatar da aikin janyo ruwa
Kogin Neja zuwa Arewa, wanda marigayi shugaba ‘Yar’aduwa ya bayar. A yau Arewa tun daga kan manyan biranenta da kauyuka da ma dukkan wani lungu da sako da ke yankin ana cikin tsananin fargaba, tsoro da rashin tabbas game da rayuwa, al’ummar yanki na cikin wahala mai gajiyarwa.
Tattalin arzikin Arewa ya mutu murus, noma da yake babbar sana’ar da al’ummar yankin ke takama da shi, amma yau ya zama tarihi. Ba jiha daya da zata iya dogara ga abin da take nomawa don ciyar da al’ummarta, duk da kasancewar akwai filayen noman masu albarka har
yanzu. Kamfanoni da Masana’antu, tuni sun durkushe, matasa da magidanata ba ayyukan yi, sai zaman kashe wando da rashin madafa. Fatara, talauci da cututtuka sun rike makogaran al’umma, yankin mune mafi ci baya ta fuskar rayuwa a zamanance, da zaran an gudanar ta wata kididdiga akan ci gaban al’umma. Wannan fili ba zai isa, a bayyana irin halin kunci da matsi da mu al’ummar Arewa muke dandana wa a bangarori da dama a cikin wannan gwamnatin. Mun ga gazawar gwamnnati akan sha’anin tafiyar da rayuwarmu.
Tsaftaceccen ruwan sha ya gagaremu, babu tsarin kiwon lafiya mai inganci, hanyoyin sufuri sun lalace, muna cikin duhun jahilci, sanadiyyar tabarbarewar harkar ilimi. Kai! Al’amura da
yawa da suka shafi zamantakewa, tattalin arziki da kuma siyasa duk mune koma baya.
A halin yanzu rikicin Boko Haram dake faruwa a yankin Arewa maso gabas, ya zame mana karfan kafa. Muna cikin damuwa da bakin ciki tare da kukan zuci da na fili, domin rashin sanin yadda makomar mu ka iya kasancewa, saboda kullum abin kara ta’azzara yake!. Tun ana
kai harin dauki dai dai, harta kai, ana zuwa gari a tarwatsashi, a kone, a kame mutanan da su kayi saura a tafi da su, kamar bayi. Gwamnatin tarayya ta ki daukar matakin da ya dace, don tsamar da yankin daga halin da yake ciki!.
Yanzu harta kai ga kame kananan hukumomi kusan guda ashirin, a jihohin Barno, Adamawa da Yobe duk da kasancewar su karkashin dokar ta baci. Mutane na ta gudun hijira, wasu su bace, wasu su mutu, yayin da sauran ke tsira cikin tagayyara da kaskanci. Daga cikin masu tserewa daga Mubi, mata hudu suka haihu a hanya, yayin da yara kusan 400 suka bace. Jinin al’ummarmu na ta kwarara dare da rana, amma gwamnati ta kawar da kanta, ko a jikin ta tamkar mu ba ‘yan kasa ba ne.
A baya an kai hari a garin Nyanya, amma shugaba Jonathan ya tsallake ya taho Kano don bikin karbar tsohon gwaman Ibrahim Shekarau, zuwa jam’iyyarsa ta P.D.P. Wani hari da aka kai makonni biyu da suka shige, mai ban tausayi a makarantar sakandare da ke Potiskum, an samu asarar rayuku masu yawa na yara dalibai. Amma gogan ko a jikinsa, sai jin sa aka yi yana bikin bayyana aniyyarsa ta sake tsayawa takarar shugabanci kasar nan a karo na biyu, maimakon zaman makoki.
Shugaba Jonathan muna tuhumarsa da nuna mana kabilanci da rashin tausayi game ta halin da mu al’ummar Arewa muke ciki. Harin bom na farko, da aka fara tayarwa a kasar nan ranar bikin ‘yancin kai, kimanin shekaru hudu a Abuja. Tsageran yankin Neja Delta sun dauki alhakin kai harin, amma Shugaba Jonathan ya kare su da cewa ba su ba ne, wanda har zuwa yau, ya ki bayyana ko su waye suka kai harin.
Mu al’ummar Arewa ba mu adawa don an hukunta wani dan Arewa idan ya yi laifi, amma da sharadin cewa idan dan Kudu, ya yi laifi makamancin wannan za a yi masa hukunci daidai da na dan Arewa. A karshe muna nusar da Shugaba Jonathan cewa tarihi baya mance komi, balle yafe laifi.
Injiniya Jibril Abdul Daura 08038997861,08022997043