Makasa sun kashe mutum biyu sun raunata daya a Gombe

Wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari gidan wani mai suna Yusuf Adamu da aka fi sani da Cooler da ke Unguwar Checheniya a garin Gombe inda suka kashe shi tare da wani makwabcinsa da ya kai masa dauki suka kuma raunata wani mutum a ranar Talatar da […]

Makasa sun kashe mutum biyu sun raunata daya a Gombe
Makasa sun kashe mutum biyu sun raunata daya a Gombe

Wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari gidan wani mai suna Yusuf Adamu da aka fi sani da Cooler da ke Unguwar Checheniya a garin Gombe inda suka kashe shi tare da wani makwabcinsa da ya kai masa dauki suka kuma raunata wani mutum a ranar Talatar da ta gabata da misalin karfe 11:45 na dare. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe DSP Fwaje Atajiri, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin ta tarho inda ya ce makasan sun kai harin ne da wasu miyagun makamai a kan shi wanda suka kashen. A cewar DSP Atajiri, a lokacin da suka kai harin sun kashe  Yusuf Adamu nan take da makwabcinsa mai suna Usman Makama, wanda ya kai masa dauki suka kuma raunata Abubakar Yayajo, wanda yanzu haka ake masa magani a wani asibiti da bai ambaci sunansa ba. Ya ce wannan hari abin takaici ne sannan sai ya kirayi al’umma cewa su rika fallasa duk wata zirga-zirgar mutanen da ba su yarda da ita ba, ya ce muddin suka fallasa irin wadannan mutanen rundunarsu za ta ba su lada ta musamman. Ya ce suna nan suna gudanar da bincike don gano wadannan makasa don gurfanar da su a gaban kuliya.