Make-maken Jona-tantin mulki

A daidai lokacin da Haurobiyawa ke jimamin tsomomuwar tsuntsun Limamin Majami’a, wanda aka makare da Dalar Hauron Amurkawa, ta yadda za a ji dadin jibgo makaman make Haurobiyawa, sai kuma Dauda-mai-maki, shugaban Majalisar Tsofaffin Haurobiya ya furta cewa babu zabi-sonka a shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje. Duk da cewa an […]

Make-maken Jona-tantin mulki

A daidai lokacin da Haurobiyawa ke jimamin tsomomuwar tsuntsun Limamin Majami’a, wanda aka makare da Dalar Hauron Amurkawa, ta yadda za a ji dadin jibgo makaman make Haurobiyawa, sai kuma Dauda-mai-maki, shugaban Majalisar Tsofaffin Haurobiya ya furta cewa babu zabi-sonka a shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje. Duk da cewa an fake da yamutsin Haramta Bobo da kwambon Bokoko, wannan dai manufa ce ta make Haurobiyawa da ke neman tsira daga sharrin Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge.
’Yan makaranta matukar ba mu kakaba wa kurungunmu tagiyar Malam Mantau ba, an taba yakin Mai tsine wa al’umma, a zamanin mulkin shugaban kasar Haurobiya mai zungureriyar tagiya, amma duk da haka sai da aka yi zabi-sonka; an yi Mushe bakanike, amma Dogo dan mutanen Daurama, ja-gaban masu fafutikar Buin-huriyya ya murkushe shi; da Janar Baban-masu gida ya dare bisa karaga, an tafka yamutsin addini a Kudancin Bayan Kada, amma duk da haka kafin ya karkare mulkinsa, sai da ya gudanar da zaben Yawon-wuni. Kai in takaice muku tun a lokacin Baba-Ojo Mai gonakin Ottawa aka fara rikicin Haramta Bobo da kwambon Bokoko, amma duk da haka sai da ya gudanar da zabi-sonka a shekara ta dubu karamin lauje da kwanciyar magirbi. Kai tun daga Jamhuriyya ta sili zuwa ta tsayuwa bisa kafa daya babu wani shugaban kasar Haurobiya da bai fuskanci tashin-tashina ba, amma wannan duk ba ta hana a gudanar da zabi sonka, matukar dai Baraden Burgar Gadi ba su hambare gwamnati ba.
Haurobiyawa, na sha furtawa a farfajiyar wannan makaranta, cewa, “mu baza na-zomo, mu zuba na-mujiya,” to karshen tika-tika tik! Kowa ya ga launin igiyoyin da ake ta tafka kulallaiya da su. Kusan komai yau ’ya’yan Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge. Sun shirya taron tarwatsa kasa, inda suka fito da kundin waskiyar kwance-tushe, don a yi tazarcen jona-tantin mulki, amma da aka fasko jirginsu, sai kawai suka shiga ‘Gudun-loko,’ ta hanyar fakewa da yamutsin Haramta Bobo da kwambon Boko da ya yi kamari a jihohin Bararon-nono da Yawon-Bebe da Damawa-fullo. Babbar manufar dai a jona-tantin mulki, ta yadda za a ci gaba da jirga Haurobiyawa, a karkashin tutar jam’iyya mai dan boto da sanda jirge.
Dauda-mai-maki ya fito kararara ya bayyana kulle-kullen da suke sakawa wajen ganin lallai ba a gudanar da zabi-sonka ba, a shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje. Kuma don su kafa wa Haurobiyawa hujja, sai Akuyar-maman-daudu, ya tashi a gaban majalisa, ya karanto sashe na sili da kofar hanci da babban lauje na kundin mulkin Haurobiya, wanda ya bijiro da batun zabi-sonka a lokacin da ake artabun yaki da kasar Haurobiya da wata kasa, inda aka yi nuni da cewa, za a kara musu wa’adin mulkin mulaka’u na tsawon watanni manuniyar sama. Lallai mu san da sani, da zarar an yi sakwa-sakwa, shagabanni sun cimma muradinsu. To za su yi ta kara wa kansu wa’adi har sa’adda Mai-duka ya fisshe mu daga sharrinsu.
Ku sani ko Karzai ya yi zabi-sonka, alhali kasarsa ta fi tamu rincabewa. Ga Pakistan su ma sun I zabi sonka. Idan har hakan ya zama dole, to muna bukatar a kafa gwamantin riwo, wadda za ta iya shawo kan masalolin da suka addabi Haurobiya, sannan ta gudanar da zabi sonka.
Don haka, a matsayina na Baban direban Alli a wannan farfajiya, ina ganin akwai bukatar mu tursasa Tumbin-wulli, ja-gaban Majalisar wakilan rafkiya, da ya yi wa su Dauda-mai-maki tawaye, ko kuma mu yi su farashin goro-goriya. Sannan ya himmatu ka’in da na’in wajen ganin a binciko azargagiyar zargin da ake yi wa Mudun sharri, tsohon Gwamna Gwaramgwam na Jihar Bararon-nono da kuma Janar Harin-jika, tsohon hafsan hafsoshin sojan Haurobiya. Shi kuwa Limamin majami’a mai tsuntsun sama, kada a sake a kyale shi, lallai a hukunta shi, idan kuwa an ki, to sai mu bijire musu.
Ku kuwa jam’iyyun adawa, matukar ba neman dawa kuke yi ba, lokaci ya yi da za ku motsa, kada a bari Dauda-mai-maki ya sake yin batanci ga Haurobiyawa, domin su yake wakilta a majalisar tsofaffi, kodayake wasu sun ce ta zama ta ‘Dattabai.’ Idan har ’yan wannan majalisar ba tababu ba ne ba, to su rika kokarin kwatanta adala, su kuma kawar da juhala. Haurobiyawa wajibi ne, mu yunkura wajen tarwatsa gungun masu fafutikar jona-tantin mulki ’yan Arewacin Haurobiya, wadanda suka hada da tsoho ‘Tanko Yakasa’ da Baffan-rawa da shekararren mutumin nan na Jihar Tumbin-Giwa.
A daidai lokacin da ake gudanar da wannan darasi na Make-maken Jona-tantin-mulki, sai kawai muka ji an kai hari Babbar Farfajiyar Horar da Direbobin Alli da ke birnin Dabo. Don haka muke son Tanko Ya-kasa ya yi mana bayani ko wadannan hare-haren na daga cikin jerin fa’idojin da suke so al’umma su ribata idan mai dan boto da sanda jirge ta ci gaba da jirga al’ummar Haurobiya?
Mu dai muna rokon Mai-duka ya la’anci mai samartakar kusu da zai yi mana sabi-zarce da adaka, ya kuma karke da runton kujera. ’Yan makaranta ku amsa, “amin!” Arewatawa sai ku kara himma wajen rokon Mai-duka tare da aikata aiki na zahiri don neman mafita da zaluncin azzalumai, masu fafutikar ganin ko ana ha maza, ha mata, sai sun yi sabi zarce.
Haurobiyawa a kakaba faden Malam Tunau, a zamanin mulkin Shugaba ’Yar’bishiya na yi muku darasin ‘Tazarce ko Ta-zame, inda na bayar da labarin masu bautar gunkin tsumburbura, har ta kai ga Shugabansu Barbushe ya bayyana musu cewa, ‘wani lokaci na zuwa, addininsu zai gushe, mulkinsu zai gushe; kabilarsu za a darkaketa.’ Saboda haka wanda duk ke bin kadin al’amuran da ke wakana na zullumin zalunci a kasar Haurobiya, in dai mai hankali a jiki nasa ne, ba mai hankali a hanun taguwa ba, zai iya yanke hukunci cewa karshen masu tafka ta’asa a kwanon tasa, don a hana mu cin wasa-wasa, na daf da cin kasa.