Makekiyar makiyayar Fullo
A makon da ya arce, wannan Farfajiya ta ragargaji sususun-wawan Makurda, kan kullin makircin da ya yi a Fadar Bila da ke Tsaunin Aso, inda muka kafa hujja da jaridar Wirkililin taronsu, wadda ta ruwaito baranbaramar gwamma gwarangwam. Don haka muke so bijiro da dabarun kirkiro da makekiyar makiyayar fullo, ta yadda za a karya […]
A makon da ya arce, wannan Farfajiya ta ragargaji sususun-wawan Makurda, kan kullin makircin da ya yi a Fadar Bila da ke Tsaunin Aso, inda muka kafa hujja da jaridar Wirkililin taronsu, wadda ta ruwaito baranbaramar gwamma gwarangwam. Don haka muke so bijiro da dabarun kirkiro da makekiyar makiyayar fullo, ta yadda za a karya lagon tada zaune tsaye, a tsakanin masu kora nagge da masu sana’ar na-duke a Jihar bini-ina-wai, da ma daukacin fadin Haurobiya.
Fullo dai ya zama wararriyar nagge, don haka sai a sace masa karsana, a hana shi kokawa. Kuma da zarar ya yi yunkuri nuna wa duniya shi ma fa ba kanwar lasa ba ne, sai a ce ya kai hari. Irin cutar da ake yi wa Fullo, duk da cewa yana samar da naman nagge da karsana da na bujimi ga kindirimo da sauran kayan dadi. Ga shi har yanzu an ki shata masa burtali ko kan iyakarsa da farfajiyar masu sana’ar na-duke. Don haka nike ganin abin da kawai ya fi dacewa ga daukacin al’ummar Haurobiya masu son a yi batu na ingarman karfen karafa, lallai sai an shata wa Fullo makekiyar makiyaya, inda zai yi ta jele tare da garken nagge da karsana da bujimi. Uwa-uba a dasa ciyawa.
Idan ba a ari faden Malam Mantau ba, a darasin da ya arce, na yi batu kan yadda kasar Danniyar-maki ta zama Makiyayar nagge da karsana da bujimi a Arewacin Turai, shi yasa ma idan an murguda baki kamar ana cin kilishi, an kuma kanga gilashi za a yi yaren Ingilishi, sai a rika kiran wannan kasa da lakabin “Northern Dairy of Europe.”
Idan har an fasko manufar Direban Allin Farfajiyar Dodorido, to ga kalubale nan ga Gwamnan Jihar Jijjiga-ciyawa, wanda na dora wa alhakin shuka ciyawar awaki da tumaki da nagge; sai baba Mai Mangwaro, wanda na dora wa alhakin shatar daji don kafa makekiyar makiyayar Fulo. Sauran shugabannin Haurobiyawa kuwa, lallai ku yi karatun watsatsaken wasikun jakin dawa da na gida kan yadda za a samar da kayan more jin dadin rayuwa, wadanda suka hada da Fura-mai-kyau ga ‘’yan dugwi-dugwi, inda za su yi ta koyon watsattsake da buda wagagen littattafai, su kuma ci gaba da kora nagge da karsana da bujimi.
Ina Hukumar bunkasa watsattsake da buda wagagen littattafai ta Fullo, ki himmatu ka’in da na’in wajen horar da ’ya’yan Fullo, ta yadda za su samu fasaha da kimiyyar bunkasa makekiyar makiyayarsu, ta zama daidai zamani, ta kuma hana waligigin zamn kashe fatari da laulayin gadin layi.
Fullo ko kun fasko cewa, Shehu Fodiye, ya yi muku wasiya kan sana’ar na-duke da kiwon nagged a karsana da bujimi da awaki da tumaki? Ku kuwa sai kuka zabi sagartu a cikin kunurmin daji, maimakon ku fahimci zamaninku, har in ta kama a cikinku a samu madugu uban tafiya, ta yadda za a rika damawa da ku a fatauci. Fullo a yi yunkurin wayewa. Ko b aka taba jin ana cewa, yau kan mage yaw aye, sai ta sha ruwa ta ci dussa.”
A nan zan karkare batutuwana da yi wa Fullo albishiri, cewa Babban Mutum Mai Rawani na birnin Shehu Mujadaddi, ya bukaci Gwamnati Jihar Bi-ni-ina-wai, ta kafa Hukumar da za ta fasko irin cututtukan da aka yi maka, amma kullum sai mujallu da makalun Bobo da kwambon Bokoko su ce kai ne mai tada kan adda, ka kai wa wasu hari, amma kai idan an sace maka nagged a karsana da bujimi babu wanda zai ji. Shi ke nan an tunkuda ka cikin kungurmin dajin kare kukanka. Fuillo na yi mafarki an yi min bushara; mafarkina ya zamto babbar ishara, sai ka zamo wani gwarzo a cikin harkokin tijara!
Sakon makaranta
Martani: Susun-Wawan-Makurda
Gaisuwa ga Babban Direban Alli, jagoran watsattsake na amintacciyar jaridar Haurobiya.
A makon da ya arce ka yi mana hannunka-mai-madoki, game da yadda Gwamna Gwaramgwam Susu-wawan-Makurda na Jihar Bini-ina-wai yake ta kurda-kurda da muguwar manufarsa ta ganin ko ta halin kaka sai ya kori Fullo daga jaharsa.
Hakika mu dai dalibai mun je gano da ke birnin kewaye, game da irin kiyayya da ake nuna wa Fullo da Hausan-kejo, ba komai ya kawo haka ba, sai kamar yadda ka furta, cewa, saboda sun kasance masu fuskantar alkibla ne tare da kadaita Mahalicci da ibada.
Ya zama wajibi ga shagabanni musamman mai-rawani na Jihar da Fullo-ke-damawa a matsayin sa na uban kungiyar Fullo Tafital-fulaku ta duniya da shugabanta na Haurobiya, wato maimakin kwarankwatsin-tsiya wato Gandun-daji, kai dama dukkanin masu fadi a kasa na-zomo aji, da su tashi tsaye don kare Fullawa da naggen Fullo.
Mu dai fatan mu masu nufin mu da sharri Allah witina moo kaidu makoo.
Daga SABIU UBA YOLA. [email protected]
07032385544
07055417766.
Shagaban jahar da fullo-ke-damawa