Makelele ya zama kocin kulob din Bastia

Tsohon dan kwallon tsakiya a kulob din Chelsea Claude Makelele ya zama kocin kulob din Bastia da ke buga wasa a gasar rukunin Ligue 1 na kasar Faransadan kimanin shekara 41, a da shi ne mataimakin Kocin PSG, Laurent Blanc da ke Faransa. Tuni mahukunta kulob din na Bastia suka sanar da daukar Makelele a […]

Makelele ya zama kocin kulob din Bastia
Makelele ya zama kocin kulob din Bastia

Tsohon dan kwallon tsakiya a kulob din Chelsea Claude Makelele ya zama kocin kulob din Bastia da ke buga wasa a gasar rukunin Ligue 1 na kasar Faransa
dan kimanin shekara 41, a da shi ne mataimakin Kocin PSG, Laurent Blanc da ke Faransa.
Tuni mahukunta kulob din na Bastia suka sanar da daukar Makelele a matsayin kocinsu a kafar sadarwarsu..
“A ranar Litinin muke sa ran kocin zai sanya hannu a yarjejeniyar da muka kulla da shi sannan a washegari za mu gabatar da shi ga duniya”, kamar yadda sanarwar da kulob din ta fitar a ranar Asabar da ta wuce ta nuna.
Makele dai ya taba yi wa kulob da dama wasa da suka hada da Celta bigo da Real Madrid a Sifen da Chelsea a Ingila da kuma kulob din PSG na Faransa.

Jami’ar Bayero ta Kano ta kori ɗalibai 78

Kotu ta yi watsi da ayyana kungiyar Palasdinawa a matsayin ’yar ta’adda

Wata matar aure ta sari mijinta da adda 

Lakurawa sun kashe fararen hula 20 a Kebbi