‘Makeri da Dila’
Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin wani makeri da dila. Labarin ya yi hani da daukar abin wai ba tare da sani ko izininsa ba.A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi. Akwai wani makeri wanda ya kasance yana gudanar da aikinsa ne […]
Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin wani makeri da dila. Labarin ya yi hani da daukar abin wai ba tare da sani ko izininsa ba.A sha karatu lafiya.
Taku; Amina Abdullahi.
Akwai wani makeri wanda ya kasance yana gudanar da aikinsa ne a cikin daji ba don komai ba sai don ba ya son hayaniya kuma idan har ya kera abu a dajin, abin ya kan yi matukar kyau saboda samun natsuwar da yake yi.
Makerin dai yana fama da matsalar beraye da ke yi masa barna a shagonsa da ke cikin dajin, don haka abun yana matukar damunsa.
Ran nan sai ya yanke shawarar bin hanyar da zai yi maganin berayen da ke damunsa. Sai ya umarci matarsa ta yi masa girkin farfesun nama, sannan ya zuba guba a ciki sannan ya kai cikin shagonsa ya bar shi a bude sannan ya kulle kuma ya yi tafiyarsa gida bayan ya gama aiki.
Can sai ga wani Dila ya tashi daga barci yana jin yunwa. Ya karade cikin daji don ya samu abinci amma abin ya cbi tura. A hanyarsa ta komawa gida sai ya ji kamshin girki yana tashi daga shagon makerin. Yana shiga shagon shagon sai ya yi ido biyu da farfesun nama, nan take ya cinye farfesun tas har da sude kwanon. Kafin ka ce kwabo cikin Dila ya kumbura kuma kafin wani lokaci ya fadi kasa yana ta shure-shure har ya mutu.
Washegari makeri na shiga shagonsa sai ya tarar da Dila a kwance a kasa ya mutu.
Da fatan Manyan Gobe sun dauki darasi a wannan labari, kada ku rika daukar kayan da ba naku ba.