‘Makeri da Dila’

Assalamu alaikum Manyan Gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin wani Makeri ne da Dila. Labarin ya yi hani da daukar abin da ba a ba ka ba. A sha karatu lafiya.   Akwai wani Makeri wanda yake gudanar da sana’rsa ta kira a daji ba […]

‘Makeri da Dila’

Assalamu alaikum Manyan Gobe tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin wani Makeri ne da Dila. Labarin ya yi hani da daukar abin da ba a ba ka ba. A sha karatu lafiya.

 

Akwai wani Makeri wanda yake gudanar da sana’rsa ta kira a daji ba don komai ba sai don ya rika samun natsuwa yana yin kira mai kyau.  Kuma a duk lokacin da ya kera wani abu, yakan yi matukar kyau.

Sai dai beraye sun sanya shi a gaba, inda suke cinye masa abubuwan da ake amfani da su wajen yin kira, tunda rumfar tasa a kungurmin daji take.

Ran nan sai ya yanke shawarar yin maganin masu yi masa barna.  Sai ya sa matarsa ta yi farfesu sannan ya zuba maganin kwari ya kai rumfarsa ya ajiye.

Can sai ga Dila yunwa ta koro shi yana yawo cikin dajin ya rasa abin da yake masa dadi. Ya zaga ko’ina bai samu abinci ba.  Da isarsa shagon makeri sai ya ji kanshin abinci yana tashi.  Nan take ya kutsa kai inda ya hau cin farfesun ba kakkautawa.

Washegari Makeri na isa shagonsa sai ya tarar da Dila a mace har ya fara kumbura.

Da fatan Manyan gobe kun dauki darasi a wannan labari.  Ka da wani daga cikinku ya rika daukar wani abu har sai ya nemi izini ko an ba shi.