Makinde ya lashe zaben Gwamnan Oyo karo na biyu

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde ya lashe Zaben Gwamnan Jihar Oyo da aka yi jiya Asabar. Gwamnan ya lashe zaben ne karo na biyu a Jam’iyyar PDP. Baturen zaben jihar, Farfesa Adedayo Bamire ne ya sanar da sakamakon zaben, inda ya ce Makinde na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 563,756, inda ya doke mai biye […]

Makinde ya lashe zaben Gwamnan Oyo karo na biyu

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde ya lashe Zaben Gwamnan Jihar Oyo da aka yi jiya Asabar.

Gwamnan ya lashe zaben ne karo na biyu a Jam’iyyar PDP.
Baturen zaben jihar, Farfesa Adedayo Bamire ne ya sanar da sakamakon zaben, inda ya ce Makinde na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 563,756, inda ya doke mai biye masa, Teslim Folarin wanda ya samu kuri’a 256,685.

Sanwo-Olu ya lashe kananan hukumomi 18 cikin 20
Akwai masu kada kuri’a 3,276,675 a jihar, wanda ke nuna ba a fito zaben ba sosai.
Gwamna Makinde ya doke fitattun abokan karawarsa guda biyu ne; Sanata Teslim Folarin na Jam’iyyar APC wanda sau uku yana sanata, da Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriy, Cif Adebayo Adelabu na Jam’iyyar Accord da sauransu.
Aminiya ta ruwaito Makinde yana cikin Gwamnoni 5 na PDP da suka yi adawa da takarar Alhaji Atiku Abubakar, inda suka koma gefe a lokaci yakin neman zabe da lokacin zaben na Shugaban Kasa.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi