Makircin Nasara a kasashen Larabawa

kasashen Yammacin Turai da Amerika sun yi amanna cewa tsarin mulkin dimokuradiyya shi ne wanda ya fi dacewa da kasashen duniya, amma sai ga shi nan suna baki biyu game da haka bisa son zuciyarsu. A bisa tsarin dimokuradiyya al’umma ne ke taruwa su tsara hanyoyi da dabarun yadda za a mulke su, da kuma […]

Makircin Nasara a kasashen Larabawa
Makircin Nasara a kasashen Larabawa

kasashen Yammacin Turai da Amerika sun yi amanna cewa tsarin mulkin dimokuradiyya shi ne wanda ya fi dacewa da kasashen duniya, amma sai ga shi nan suna baki biyu game da haka bisa son zuciyarsu. A bisa tsarin dimokuradiyya al’umma ne ke taruwa su tsara hanyoyi da dabarun yadda za a mulke su, da kuma zaben mutanen da suka dace su wuce gaba a dukkan al’amuran da suka shafi jama’a da kuma amincewa da yanayin madafun ikon da suka kamata a yi amfani da su. A takaice dai wanan shi ne daidai da yadda Turawan suke ayyanawa cewa dimokuradiyya salon mulki ne na jama’a domin jama’a bisa abin da jama’a ke bukata. Haka ne kasashen duniya ke ta amfani da wanan tsarin tun daga lokacin da aka kirkire shi a kasar Girka fiye da shekaru dubu hudu da dari biyar.
To a yanzu idan har turbar dimokuradiyyar da wata kasa za ta bi ta sha bamban da irin wacce Amurka da kawayenta ke kai, to tabbaci hakika za su nuna cikakkiyar adawarsu game da haka, duk kuwa da cewa kasashen duniya a wannan marrar ‘yantattu ne, suna da zabin yin dimokuradiyyar da suka ga cewa ita ce za ta fisshe su. A ‘yan kwanakin nan mun ga yadda aka takura wa Shugaba Robert Mugabe saboda bin tafarkin dimokuradiyyar da jama’ar kasar Zimbabwe suka tsara, suka kuma bi, hakan kuma ya kai su ga nasara. Haka nan kuma a yanzu muna ganin yadda wadannan kasashen ke neman canja ma’anar dimokuradiyya a kasar Masar  ba kamar yadda jama’ar kasar suka bukata ba.
Wannan babban abin kunya ne, ganin yadda Turawa ke katsalandan a cikin harkokin kasashen da ba sa ra’ayin dimokuradiyya irin tasu, musamman ma wadanda ba su da karfin kare kawunansu daga sharrinsu, ba su kuma da halin tsoma baki cikin harkokin wadancan kasashen.  Dangane da haka ana iya cewa abubuwan da ke faruwa a kasar Masar babban koma-baya ne  ga masu fafitukar karfafa dimokuradiyyar da Turawa ke tunkaho da ita. Abin da ya faru a kasar Masar juyin mulki ne don dakile gwamnatin da aka samar bisa tafarkin dimokuradiyya, kuma abin da ke nan kasashen Amurka da Turai ke kwarmato akai a duk lokacin da aka yi  haka a wata kasa, har ma sukan turza don kuntata wa wadanda suka yi juyin mulkin don a mayar da mulkin ga wadanda aka kwata daga gare su,  ko kuma su shiga uku.
A sakamakon wannan al’amarin da Turawa suka daure gindin afkuwarsa, suka kuma kasa hukunta wadanda suka assasa shi, yakin basasa na iya barkewa a kasar Masar wacce ta kasance jagorar sauran kasashen Larabawa, domin kuwa juyin mulkin da aka yi a kasar ba shi ne hanyar warware matsalar da Yahudawan da Amurka ta daure wa gindi suka haddasa don ganin bayan addinin Musulunci ba. Baicin haka nan abin takaici ne ganin yadda wasu kasashen Larabawa da ke kawance da Amurka suka ki goyon bayan Shugaba Morsi da aka hambarar, bisa zarginsa da  kokarin kawo siyasar addini a kasar, domin samun nasarar da jam’iyyarsa ta Ikhwanul-Muslimin (‘Yanuwa Musulmi)  ta yi na shimfida tsarin da zai ba mafiya rinjayen al’umman kasar Masar damar kare mutuncin addininsu
An dai tabbatar cewa ba wani abu ba ne ya sa aka hambarar da Morsi illa tsarin da ya yi na gudanar da zaben raba gardama bisa kundin tsarin mulkin da zai share fagen yin amfani da shari’ar Musulunci a kasar da kuma bunkasar manufofin kungiyar ‘Yanuwa Musulmi kamar yadda suka tsara a sabon kundin tsarin mulkin kasar da sojoji suka hambarar.
Idan da gaske Turawa ke yi game da karfafa tsarin dimokuradiyya a kasashen duniya, me ya sa ba za su matsa wa sauran kasashen Larabawan da ke Jaziratul Arabiya bin tafarkin dimokuradiyyar da suka tsara da kansu don amfaninsu ba? A’a ba dimokuradiyar  ce ta dame su ba, yadda za su kare muradunsu ne a kasashen Larabawa ya fi damunsu. Shi ya sa suka buge  da rarraba kawunan al’ummomin kasashen Larabawa bisa addinin Musulunci, don su samu damar haddasa yanayin da zai ba su daman tsoma baki cikin harkokin kasashen. Dangane da haka ne suke goyon bayan Musulmin Sunni a wasu kasashe, suna kuma kuntata wa ‘yan Shi’a a wasu kasashen. Goyon bayansu ga Musulmi ya dogara ne bisa ra’ayinsu da kuma abin da za su tatsa ko kankara daga al’ummomin kasashen. Muddin dai kasashen Larabawa ba su fahimci haka ba, suka komo daga rakiyar su, to ba makawa za su ingiza Isra’ila afka wa kasashen Larabawa a fakaice alhali Amurka ce za ta yake su, kamar yadda aka yi niyyar yi yanzu a kasar Syria.