Makiya Musulunci ne ke tada rigima a Arewa – Walin Kalgo

Tsohon limamin sojoji a zamanin mulkin Janar Murtala Muhammad, Malam Abubakar Atiku (Walin Kalgo), ya yi zargin cewa rigingimun da ke faruwa a Arewa da sunan addini sharri ne na wadansu makiya addinin Musulunci.Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Bunza, inda ya yi kira ga Musulmi da […]

Makiya Musulunci ne ke tada rigima a Arewa – Walin Kalgo
Makiya Musulunci ne ke tada rigima a Arewa – Walin Kalgo

Tsohon limamin sojoji a zamanin mulkin Janar Murtala Muhammad, Malam Abubakar Atiku (Walin Kalgo), ya yi zargin cewa rigingimun da ke faruwa a Arewa da sunan addini sharri ne na wadansu makiya addinin Musulunci.
Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Bunza, inda ya yi kira ga Musulmi da su guji duk wata al’ada da ta saba wa karantarwar Musulunci ko kuma duk abin da ke kawo batanci ga addinin.
“Babu Musulmin kirki da zai iya daukar makami ko bom ya hallaka dan uwansa da kuma kansa da sunan Musulmi saboda addinin Musulunci bai koyar da haka ba. Kamar yadda kowa ya sani, addinin Musulunci, addini ne na zaman lafiya. Ni dai a tunanina, akwai wata makarkashiya da ya zama dole shugabanninmu su tsananta bincike don gano bakin zaren.” Inji shi.
Ya kara da cewa, “ba zan yarda cewa Musulmin kwarai ne ke tayar da bama-bamai da kuma yi wa mutane kisan gilla a nan Arewa ba, domin Alkur’ani ko Hadisan Annabi (SAW) ba inda suka koyar da haka. Idan babu lauje cikin nadi, babu yadda za a ce, sojojinmu sun kasa murkushe su acikin dan kankanen lokaci.”
A karshe, tsohon limamin sojojin ya yi kira ga al’ummar Musulmi, musamman matasa su tashi tsaye wajen neman ilimi, musamman na addini don kare martabar addinin Musulunci da Musulmi.
Bashir A. Zakka, a Birnin Kebbi
Tsohon limamin sojoji a zamanin mulkin Janar Murtala Muhammad, Malam Abubakar Atiku (Walin Kalgo), ya yi zargin cewa rigingimun da ke faruwa a Arewa da sunan addini sharri ne na wasu makiya addinin Musulunci.
Malamin ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a garin Bunza, inda ya yi kira ga Musulmi da su guji duk wata al’ada da ta saba wa karantarwar Musulunci ko kuma duk abin da ke kawo batanci ga addinin.
“Babu Musulmin kirki da zai iya daukar makami ko bom ya hallaka dan uwansa da kuma kansa da sunan Musulmi saboda addinin Musulunci bai koyar da haka ba. Kamar yadda kowa ya sani, addinin Musulunci, addini ne na zaman lafiya. Ni dai a tunanina, akwai wata makarkashiya da ya zama dole shugabanninmu su tsananta bincike don gano bakin zaren.” Inji shi.
Ya kara da cewa, “ba zan yarda cewa Musulmin kwarai ne ke tayar da bama-bamai da kuma yi wa mutane kisan gilla a nan Arewa ba, domin Alkur’ani ko Hadisan Annabi (SAW) ba inda suka koyar da haka. Idan babu lauje cikin nadi, babu yadda za a ce, sojojinmu sun kasa murkushe su acikin dan kankanen lokaci.”
A karshe, tsohon limamin sojojin ya yi kira ga al’ummar Musulmi, musamman matasa su tashi tsaye wajen neman ilimi, musamman na addini don kare martabar addinin Musulunci da Musulmi.

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi

NDLEA ta kama miyagun ƙwayoyi tan 3.9 da kama mutum 599

An kashe ’yan gudun hijira uku a Sakkwato