Makiya sun sanya ni a gaba – Zainab Indomie

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Zainab Abdullahi wadda aka fi sani da Zainab Indomie ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ta rasu dalilin matsananciyar rashin lafiyar da ta yi fama da ita.A lokacin da jarumar take yi wa Aminiya karin bayani ta wayar salula, ta ce a yanzu tana samun sauki sakamakon matsananciyar rashin lafiyar […]

Makiya sun sanya ni a gaba – Zainab Indomie
Makiya sun sanya ni a gaba – Zainab Indomie

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Zainab Abdullahi wadda aka fi sani da Zainab Indomie ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ta rasu dalilin matsananciyar rashin lafiyar da ta yi fama da ita.
A lokacin da jarumar take yi wa Aminiya karin bayani ta wayar salula, ta ce a yanzu tana samun sauki sakamakon matsananciyar rashin lafiyar da take fama da ita, sannan ta bayyana cewa makiyanta ne suka yi uwa da makarbiya kan rashin lafiyar da take fama da ita.
Ta ce: “Ka san idan ka samu daukaka, za a zuba maka idanu, musamman ma da na kasance daya daga cikin jaruman fina-finan Hausa masu farin jini. Wadannan makiya ba sa son ci gabana, sun san idan har ina da cikakkiyar lafiya ba za su yi rawar gaban hantsi a gabana ba. Burinsu a yau a ce babu ni, to ta Allah ba ta tasu ba, domin ina kara samun sauki.”
Duk da cewa jarumar ta ki bayyana wa Aminiya cutar da take damunta, amma ta tabbatar da cewa a kwanankin baya ta samu kanta cikin halin tasku. “Har na fara fitar da rai a kan ko zan rayu, dalilin wata cuta da take damu na, amma a yanzu na gode wa Allah, ina samun sauki. Nan gaba kadan ma za a ci gaba da gani na a fina-finai.” Inji ta.
Ta gargadi makiyanta cewa ba su isa su yi mata abin da Allah bai kaddara zai faru da ita ba. Sannan ta yi wa masu watsa jita-jita nasiha, da su daina watsa labarun karya, domin hakan ba zai haifar musu da da mai ido a ranar sakamako ba.
A karshe ta gode wa masoyanta da suka kasance da ita a lokacin da take cikin dadi da kuma tsanani, sannan ta bukaci jama’a su ci gaba da yi mata addu’a don ta samu ingantacciyar lafiya, ta kuma fi karfin makiyanta.