Makiyan Kwankwaso ke neman a kwace kujerata —Abba
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi zargin cewa neman kwace kujerersa da ma duk matsalolin da yake samu a siyasa, ba komai ba ne face shirin makiya na karya uban gidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi zargin cewa neman kwace kujerersa da ma duk matsalolin da yake samu a siyasa, ba komai ba ne face shirin makiya na karya uban gidansa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Abba ya yi wannan furucin ne a wani a taron masu ruwa da tsaki na tafiyar Kwankwasiyya a Kano, wanda shi ne karon farko tun bayan da Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta tabbatar da hukuncin kwace kujerar gwamnan jihar daga hannunsa.
Kwankwaso ne ya kira taron, wanda cikin mahalartansa hadar da mataimakin gwamna, Aminu Abdussalam da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Ismail Falgore da dan Majalisar Tarayya mai wakilai Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin Kofa da shugabannin Jam’iyyar NNPP da kwamishinoni da kuma manyan jami’an gwamnatin Kano.
Gwamna Abba ya shaida wa taron cewa, “Za mu ci gaba da biyayya ga Kwankwaso wajen yin abin da ya dace da yardar Allah. Wajibi ne mu gode wa Kwankwaso mu kuma kara shaida masa cewa shi abin alfaharinmu ne.
- Shin Hukuncin Kotuna Kan Zaben Gwamnoni Ya Sauya Dimokariɗiyya?
- An kama matashi kan zargin luwadi da dan shekara 4 a Gombe
“Ko da duniya za ta hana mu komai saboda da manufofinsa, ba za mu juya masa baya ba ko mu juya wa manufofinsa baya.”
Gwamnan Abba Kabir ya bukaci jagororin NNPP kada su karaya ko su tayar da jijiyoyin wuya da kowa, maimakon haka su mayar da hankalinsu wajen ba wa Kanawa kwarin gwiwa.
Ya kuma yi alkawarin dorawa kan muhimman ayyukan cigaban al’umma da ya faro, da suka kunshi ba da kulawa ta musamman ga mata da kananan yara da kuma biyan hakkokin ’yan fansho.