Makiyaya a Otukpo sun ba da hadin kai ga dokar kiwo
Makiyaya a karamar Hukumar Otukpo dake Jihar Benuwai sun ba da hadin kai wajen yin aiki da dokar kiwo wacce gwamnatin jihar ta aiwatar, inda ta samar da dajin da makiyayan za su rika kiwo ba tare da fita da yankin ba. Dokar kiwon wacce ta fara aiki tun ranar 1 ga watan Nuwambar nan, […]
Makiyaya a karamar Hukumar Otukpo dake Jihar Benuwai sun ba da hadin kai wajen yin aiki da dokar kiwo wacce gwamnatin jihar ta aiwatar, inda ta samar da dajin da makiyayan za su rika kiwo ba tare da fita da yankin ba.
Dokar kiwon wacce ta fara aiki tun ranar 1 ga watan Nuwambar nan, ta janyo cece-kuce mai yawan gaske a kasar nan, lamarin da sanya wasu makiyayan kauracewa jihar baki daya tare da dabbobin nasu. Domin an ruwaito cewa Fulani sun tasa keyar shanunsu kimanin miliyan 10 daga Jihar Benuwai zuwa Jihar Nasarawa a makon da ya gabata don kaucewa abinda suka kira takunkumi kamar yadda Shugaban kungiyar Miyatti-Allah Cattle Breeders, Alhaji Musa Muahhed-Mati.
Amma Fulani makiyaya dake Utukpo sun yanke hukuncin baiwa dokar kiwon hadin kai, inda suka bada tabbacin ci gaba da zama tare da gudanar da harkokinsu na kiwo da kasuwanci da sauransu a yankin.
Babban basaraken Gargajiya na Otukpo, if John Eimonye ya bayyana wa manema labarai cewa makiyaya a yankinsa sun bada cikakken hadin kai wajen yin aiki da dokar da Jihar Benuwai ta kafa kan ka’idojin kiwo a jihar. Haka kuma basaraken ya kara da cewa hadin kan da Fulani makiyayan suka bayar ya kai kashi 80 cikin 100, sannan ya cewa ci gaba da zaman fulanin a yankin nasa zai kara kawo cigaba ga jama’arsa tare kuma da wanzar da zaman lafiya.
“Ni kaina da Shugaban karamar Hukumar Otukpo da shugabannin fulanin mun zauna mun tattauna akan muhimman kalubalen da ake fuskanta. Mun ganom cewa babu isasshen ruwan da zai wadaci dabbobin nasu a wannan hurumin, wannan ya sanya muka bada karin lokaci na sa’o’I biyu a kullum da za su rika fitowa don shayar da dabbobinsu ruwa sannan su koma.
“Don haka nake cewa matakin hadin da aka samu tsakin makiyaya da shugabannin yankin nan ya kai kashi 80 cikin 100. Daga yanzu babu sauran jidalin yawo da shanu ko’ina kamar da. Sannan sun bukaci karin filin kiwon kuma kan wannan bukata mun kafa kwamitin da zai duba yadda zai samar da masu kafin nan da watanni biyu,” a cewar basaraken.
Haka kuma babban ardon Fulani na yankin, Alhaji Risku ya bayyana cewa, sun baiwa hukumomin yankin tabbacin cewa za su aiki da sababbin dokokin kiwo a yankin da zarar an nuna masu hurumin da shanun nasu za su kasance cikinsa. Ya kuma kara da cewa, a yayin da suke ci gaba da tattaunawa da hukumomin yankin, suna fama da matsalar isasshen ruwan shan dabbobinsu da bigiren kiwon kansa kasancewar an hana yawatawa ko’ina kamar da, amma dai ya ce babban abu gaba daya shi ne yadda suke zaune lafiya da kowa a yankin bajki daya.
Kodinetan Miyetti-Allah Cattle Breeders na Najeriya reshen Jihar Benuwai MACBAN), Garus Gololo ya kara tabbatar da wannan hadin kai da aka samu tsakanin Fulani da hukumomin Otukpo da Guma, inda ya ce komai na tafiya yadda ya kamata cikin lumana da fahimtar juna.