Makiyaya: Ba filin mutane za a kwace ba – Gwamnatin Kaduna

dahiru Abdu shi ne jami’in hulda da jama’a na Ma’ikatar gona ta jahar Kaduna, ya ce kafin gwamnatin tarayya ta fito da wannan tsari tuni mu a Jihar Kaduna mun fara wannan tunani. Saboda haka mu har yanzu ba mu samu wata tirjiya daga wani yanki a jahar Kaduna ba dangane da lamarin, saboda abu […]

Makiyaya: Ba filin mutane za a kwace ba – Gwamnatin Kaduna
Makiyaya: Ba filin mutane za a kwace ba – Gwamnatin Kaduna

dahiru Abdu shi ne jami’in hulda da jama’a na Ma’ikatar gona ta jahar Kaduna, ya ce kafin gwamnatin tarayya ta fito da wannan tsari tuni mu a Jihar Kaduna mun fara wannan tunani. Saboda haka mu har yanzu ba mu samu wata tirjiya daga wani yanki a jahar Kaduna ba dangane da lamarin, saboda abu ne da kowa ya san  zai taimaka a samu zaman lafiya, domin zai kawo karshen tashin hankali tsakanin makiya da manoma. Ko mutanen yankin  kudancin Kaduna suna farin ciki da wannan tsari na gwamati, ni a iya sanina ba mu samu wani da ya fito fili ya ce wai baya son abin ba.
‘’Gaskiya ban da masaniya a nan dai jahar cewa wai wadansu ba sa kaunar wannan tsarin, sai dai kila wani bangare na kasar nan, amma a nan Kaduna dai kam har yanzu ba mu ji wanda ya fito ya ce wannan tsari da za ayi bai da ce ba.’’
Ya ci gaba da cewa, ‘’Abin da muke son jama’a su sani shi ne, ba fa cewa aka yi za a killace wadansu mutane a filinsu  ba ne, a’a hatta ciyayi da sauran abubuwan more rayuwa ana da shirin samar wa mutanen a wajen. Ba kuma cewa aka yi za a kwace wa mutane fili ba ne domin girke wadansu mutane a wajen ba. Hatta makaranta da kasuwa da sauran irin wadannan ababe ana da niyyar samar wa a wajen, domin wata makiyaya ce ake son kafawa domin rage yawace-yawacen makiyaya. Za a kuma bai wa ‘ya’yansu shanu domin kiwo, saboda haka ba wai ana nufin killace wadansu mutane ba ne a filin wadansu mutane ba, ba haka shirin ke nufi ba.’’
Ya ce, ‘’Mafi yawan  mutane ba su fahimci wannan tsari ba,  ko abin da gwamnati ke nufi ba, har suke ganin kamar za a kwasu wadansu fulani ne a girke masu a filaye, kamar wasu ‘yan gudun hijira. Gwamnati na shirin samar da waje ne domin a ja hankalin makiyaya su zauna, a maimakon su rika zuwa yawon kiwo har a rika samun rikice-rikice tsakaninsu da manoma. Akwai maganar shuka ciyawa ma domin dabbobin su rika samun abinci.’’
“Misali, bafullatani ya samu ciyawa ingantacce da rowan sha, sannan an biyo shi inda yake an ba shi kayan more rayuwa, ka ga ai za a samu saukin fitina da kuma satar shanu. Har ila yau, wannan zai taimaka a rika gane idan bakin fulani sun shigo cikin kasa ko gari, wanda a yanzu ba a ganewa. Saboda haka muna jawo hankalin mutane da su fahinci manufar ita gwamnati a kan wannan batu. Ba filinsu za a kwace ba, so ake yi kawai a samo maslaha a game da rikicin manoma da makiyaya a kasa.’’
Sai dai kuma wani dan Majalisar Tarayya mai wakiltar gundumar kaura,   Gideon Gwani, ya yi Allah wadai da kokarin da gwamnatin jahar Kaduna take yi na samar da makiyaya a kudancin jahar, inda ya ce ba a tuntube mutanen yankin ba.
Ya bayyana ra’ayinsa ne a zantawa da ya yi da wata kafar watsa labarai ta yanar gizo a Kaduna.
Ya ce, duk da cewa  dokar kasa sashe na   43 ya bai wa gwamnatin jahar damar mallakar filaye, amma sashe 202 na dokar kasa ya ce dole gwamnati ta amince da ra’ayin jama’a.” Idan kuwa haka ne, ke nan jama’a sun zama masu ruwa da tsaki a kan al’amuran da suka shafi filaye. Don haka akwai bukatar gwamnati ta saurari ra’ayoyin mutane da na yankunansu a kan al’amuran da suka shafi yin amfani da fili ko kasa,” inji shi.
Gwani ya ce, al’ummar  kudancin Kaduna manoma ne ba makiyaya ba, don haka kamata ya yi gwamnati ta samar wa jama’ar  yanki tsarin da ya dace da su.