Makiyaya ba za su taba amincewa da dokar hana kiwo a Najeriya ba – Gan Allah

Kungiyar Ci Gaban Al’ummar Fulani ta Gan Allah ta Najeriya ta ce al’ummar Fulani makiyaya na Najeriya, ba za su taba amincewa da kafa dokar hana kiwo a kasar nan ba. Kungiyar ta bayyana haka ne a takardar sanarwar bayan taronta na kasa da ta gudanar a garin Kaduna. Da yake karanta takardar bayan taron […]

Makiyaya ba za su taba amincewa da dokar hana kiwo a Najeriya ba – Gan Allah

Shugabannin Qungiyar Fulani ta Gan Allah ta Najeriya

Kungiyar Ci Gaban Al’ummar Fulani ta Gan Allah ta Najeriya ta ce al’ummar Fulani makiyaya na Najeriya, ba za su taba amincewa da kafa dokar hana kiwo a kasar nan ba.

Kungiyar ta bayyana haka ne a takardar sanarwar bayan taronta na kasa da ta gudanar a garin Kaduna.

Da yake karanta takardar bayan taron Shugaban Kungiyar na Kasa, Alhaji Sale Bayeri ya ce kamar yadda kowa ya sani ne tsarin mulkin Najeriya, ya bai wa kowanne dan Najeriya ’yanci ya yi walwala ya shiga duk inda ya ga dama a kasar nan.

Ya ce, amma don raina hankali, yau sai aka wari gari aka ce wasu jihohin Najeriya sun kafa dokar hana Fulani kiwo.

“Bafulatani bai taba tunanin cewa, wata rana za a hana shi kiwo a Najeriya ba. Bafulatani bai san wata sana’a ba, sai kiwon dabbobinsa don haka babu abin da yake so, sai dai a bar shi ya ci gaba da kiwon dabbobinsa a daji da ya gada daga iyaye da kakaninsa,” inji shi.

Alhaji Bayeri ya ce, duk wanda ya kawo shawarar a hana Fulani kiwo a Najeriya yana kokarin hallaka al’ummar Fulani ne. Kuma al’ummar Fulani ba za su tsayawa suna kallon a hallaka su ba.

Ya ce, idan  ana son a zauna da al’ummar Fulani lafiya a Najeriya a bar  su yi sana’ar  da suka gada daga iyaye da kakanni.

“Za su ci gaba da yaki kan wannan doka ta hana kiwo, da wasu jihohi suka kafa a Najeriya. Hadari ne gwamnatin Najeriya ta bar wata jiha ta kafa dokar hana kiwo,” inji shi.

Ya ce, “Muna gaya wa gwamnati idan ba za ta tsare mu ba, za mu tsare kanmu. Domin dokar Najeriya da dokar Majalisar Dinkin Duniya sun bai wa kowanne dan Najeriya hurumin ya kare kansa idan har gwamnati ta gaza kare shi. Gwamnatin Najeriya ba ta kare al’ummar Fulani. Don haka muna fada wa gwamnatin Najeriya ta kare al’ummar Fulani.”

Alhaji Bayeri, ya ce yau rikici tsakani Fulani makiyaya da manoma ya cinye dabbobin Fulani kashi 35 cikin 100. Kuma duk tallafin da gwamnatin Najeriya ke yi ga manoma kawai take yi ba ta taba tallafa wa makiyaya ba.

Bayeri ya ce, a Najeriya a kowace rana ana cin dubban shanun da Fulani makiyaya suke samarwa. Ya ce ba don shanun da Fulani makiyaya suke samarwa a Najeriya ba, sai gwamnati ta dauki biliyoyin Naira ta kashe wajen shigo da shanu zuwa kasar nan.

“Gwamnati ta tallafa wa manoman da suka yi asara da Naira biliyan 84 sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi a bara. Kuma ta tallafa wa manoman shinkafa da Naira biliyan 60. A cikin shekara 3 da suka wuce Fulani makiyaya  sun yi asarar mutum sama da 2,700 da shanu sama da miliyan 3, a  jihohin Taraba da Benuwai da Filato da Kudancin Kaduna da Kwara da Kogi da Zamfara da Sakkwato da Katsina. Amma babu wata gwamnati tunda daga karamar hukuma da jihar da  ta tarayya da ta tallafa wa Fulani makiyaya kan wannan asara da suka yi,” inji Bayeri.

Bayeri, ya ce yau  ’ya’yan Fulani sama da dubu 3 ne  suke tsare a gidajen kurkuku da ofisoshin ’yan sanda a Najeriya. Ya ce, a shekara 20 da suka gabata babu ’ya’yan Fulani 300 a gidajen kurkuku. Saboda ba a hana su sana’ar da suka gada iyaye da kakanni ba. Sai ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi wa ’ya’yan Fulani makiyaya da suke tsare a gidaje kurkukun kasar nan afuwa, kamar yadda aka yi wa ’yan Neja-Delta.

Ya ce, al’ummar Fulanin Najeriya da suka kai miliyan 25, suna son a yi taron gyara fasalin kasa don  bai wa al’ummar Fulani da sauran al’ummomin Najeriya damar  bayyana abubuwan da suke so.