Makiyaya biyu sun samu tabin hankali don gwanjon shanunsu

Makiyaya biyu daga cikin makiyaya 10 da ake zargin Alkali Aminu Kagara da yin gwanjon shanunsu 259 da awaki da tumaki 189 da aka sayar kasa da Naira miliyan 10 sun samu tabuwar hankali.Wata biyar da suka gabata ne alkalin ya yi gwanjon dabbobinsu, wanda hakan ya jefa rayuwarsu a cikin kunci, kamar yadda binciken […]

Makiyaya biyu sun samu tabin hankali don gwanjon shanunsu
Makiyaya biyu sun samu tabin hankali don gwanjon shanunsu

Makiyaya biyu daga cikin makiyaya 10 da ake zargin Alkali Aminu Kagara da yin gwanjon shanunsu 259 da awaki da tumaki 189 da aka sayar kasa da Naira miliyan 10 sun samu tabuwar hankali.
Wata biyar da suka gabata ne alkalin ya yi gwanjon dabbobinsu, wanda hakan ya jefa rayuwarsu a cikin kunci, kamar yadda binciken wakilinmu ya gano.
Makiyayan su ne Chumu, dan shekara 25 da Hori mai shekara 27 da suke zaune da matansu da ’ya’yansu a Kodo, karamar Hukumar Wushishi a Jihar Neja, gwanjon da Alkali Aminu Kagara ya yi ya sa Chumu ya rasa shanu 23 da tumaki da awaki 18, sai Hori shanu 27 da tumaki da awaki 21.
Chumu, wanda Malam Haruna Suleiman Utono ya shaida wa Aminiya cewa mutum ne mai kaifin basira wurin gudanar da harkokinsa, yanzu bai iya bambance Naira 5 da Naira 1,000.
Makiyayan 10 an gwanjatar da dabbobinsu ne saboda hukuncin da Alkali Aminu Kagara ya yanke na biyan diyyar hannun Faruku, mai kimanin shekara 20, wanda danbaba ya sare wa hannu da adda sakamakon sabanin da suka samu da wan danbaba din.
Malam Haruna Utono ya ce Faruku ya rasa hannunsa ne bayan da suka sari junansu da adda, lokacin da Faruku da abokinsa suka je wurin danbaba yayin da ake bikin Gwarawa suka ja shi da magana, abokin Faruku ya rabka wa danbaba sanda aka, shi kuma Faruku ya sare shi da adda a hannu.Ganin haka sai danbaba ya sari Faruku da adda, lamarin ya sa mahaifin Faruku Alhaji Auta ya kai shi a yi masa magani.
Ya ce mahaifin Farukun ya nemi iyayen danbaba su dauki nauyin jinyar da dansa a wurin magani inda aka kashe Naira dubu 80. Bayan haka, ya nemi a biya su kudin dorin da aka yi a hancinsa zuwa Naira dubu 120. Sun kuma nemi a ba su kudi su saya masa hannun roba kan Naira dubu 500, daga baya suka nemi a kara musu Naira dubu 100.
Aminiya ta samu bayanin cewa duk da biyan wadannan makudan kudi, bayan wata takwas Alhaji Auta ya shigar da kara gaban kotun Alkali Aminu Kagara a garin Zungeru a karamar Hukumar Wushishi.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah, reshen Jihar Neja, Alhaji Isma’ila Ahmad Rebe ya yi tsayin daka don sasanta bangarorin biyu domin kada a dauki matakin da bai dace ba, ganin jama’a na iya daukar doka a hannu. Matakin da ya sa aka biya kudin jinya da dori da na hannun roba da kuma wasu Naira dubu 100 da suka nema jimilla sun kashe Naira dubu 828.
Alhaji Isma’ila Rebe ya shaida wa manema labarai cewa al’amarin ya shafi makiyaya magidanta bakwai da matasa uku, inda aka buga lissafin kudin dabbobin ba su kasa Naira miliyan 28 da dubu 900 ba, amma ga shi an yi gwanjonsu kan kudin da bai haura Naira miliyan takwas ba.
Alhaji Muhammad Abubakar Sadik shi ne Babban Daraktan Harkokin Makiyaya a Ofishin Gwamnan Jihar Neja, ya shaida wa Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu halin da ake ciki inda ya umurci Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Abdullahi Bawa ya dauki matakan da suka kamata kan lamarin.
Aminiya ta gano tun a watan Afrilun bana ne Gwamnatin Jihar ta nada kwamitin da zai binciki lamarin a karkaashin Mai shari’a Halima Ibrahim kuma a watan jiya ne aka nemo wakilan makiyayan da Alkali Aminu Kagara da lauyan masu kara Ibrahim Liman Wushishi gaban kwamitin kuma ba su musanta zargin da aka yi musu ba kan lamarin.
Yanzu haka aure tsakanin yayar Faruku da mijinta na tangal-tangal, saboda shanunsa 45 da awaki 35 na cikin wadanda alkalin ya yi gwanjo.
Shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta Cibil Right Congress, wadda ta samu labarin ta gidan Rediyon Muryar Amurka, Kwamred Shehu Sani ya tuntubi makiyayan don taimaka musu wajen kwato musu hakkinsu, inda yanzu haka ya fara shirye-shiryen tunkarar gwamnatin jihar, don ganin an biya makiyayan 10 da aka yi wa awon gaba da dabbobinsu.