Makiyaya na fama da matsalar rayuwa a Abuja – Sarkin Fulani
Wani jagoran Fulani a yankin birnin tarayya Abuja, Alhaji Ibrahim Shekarau ya koka akan matsaloli da al’ummarsu ke fuskanta a yayin kiwo a yankin birnin tarayyar, bayan mayar da wuraren da a ka tanada masu zuwa gonaki. Shekarau wanda shi ne Sarkin Fulanin Lugbe Abuja, ya ce gwamnatin mulkn soja ta Ibrahim Babangida ta tanadar […]
Wani jagoran Fulani a yankin birnin tarayya Abuja, Alhaji Ibrahim Shekarau ya koka akan matsaloli da al’ummarsu ke fuskanta a yayin kiwo a yankin birnin tarayyar, bayan mayar da wuraren da a ka tanada masu zuwa gonaki. Shekarau wanda shi ne Sarkin Fulanin Lugbe Abuja, ya ce gwamnatin mulkn soja ta Ibrahim Babangida ta tanadar masu wuraren kiwo a kusurwowin Abuja uku da suka hada da dajin Kawu dake Bwari da Paikon-Kore a Gwgwalada sai kuma wani wurin kiwon a yankin Karshi dake AMAC, amma kuma a cewarsa babu damar su yi kiwo a wuraren sakamakon rashin tabbatar masu da wuraren, inda wasu ke yin noma a ciki.
Haka nan ya ce a baya ga makiyayan na yin kiwo a dazuzzuka dake kusa da garuruwan yankin, amma a yanzu hakan bai yiwuwa kasancewar inji shi al’ummar Gwari da sauran kabilun yankin na shuka itatuwan kashu a cikinsu don cin moriyar diyya a duk lokacin da ayyukan gine-gine suka iso wuraren. “Sannan idan makiyaya su ka matsa zuwa dazuka da ke nesa da gari sai a rika garkuwa da su a na neman kudin fansa,” in ji shi.
“A dalilin hakan mun gwammace yin kiwo a wuraren da ke da ciyawa a cikin garuruwa amma a nan din ma sai jami’an duba-gari su kama wasu daga cikin shanunmu su tafi da su zuwa kotunan tafi da gidanka inda a ke cin tararsu dubban naira a kan kowane shanu guda. Wannan gwamnatin ta taimaka mana a bangaren yaki da masu kai hari a rugage su na kashe mana al’umma tare da kora dabbobinsu a saboda haka mu na kira ga mai girma Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello da ya kawo mana dauki a bankaren wuraren kiwo don samar da karin zaman lafiya a birnin,” inji sarkin Fulani.