Makiyaya na shirin kai alkalin da ya yi gwanjon shanunsu gaban kotu
Makiyaya 10 da tsohon Alkalin Kotun Shari’ar Muslunci ta Zungeru Alkali Aminu Kagara ya yi gwanjon dabbobinsu don biyan diyya na shirye-shiryen gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Minna, domin neman a bi musu hakkinsu.Kakakin makiyayan Malam Haruna Suleiman Utono ne ya shaida wa wakilinmu haka ta waya, bayan da Hukumar […]
Makiyaya 10 da tsohon Alkalin Kotun Shari’ar Muslunci ta Zungeru Alkali Aminu Kagara ya yi gwanjon dabbobinsu don biyan diyya na shirye-shiryen gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Minna, domin neman a bi musu hakkinsu.
Kakakin makiyayan Malam Haruna Suleiman Utono ne ya shaida wa wakilinmu haka ta waya, bayan da Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar Neja ta sallami Alkali Aminu Kagara daga aiki bayan karbar rahoton kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ya binciki lamarin gwanjon dabbobin.
Malam Haruna Utono ya ce tuni suka kira lauyansu domin daukar matakan da suka kamata, don ganin kotu ta kwato musu dukiyarsu da tsohon alkalin ya salwantar da kuma neman biyansu diyyar sanya rayuwarsu a kunci har biyu daga cikinsu suka tabin hankali.
Ya yaba wa kwamitin karkashin Mai shari’a Halimah Ibrahim Abdul-Malik kan gudanar da aikinsa bisa adalci.
Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Jihar Neja Barista Abdullahi Bawa ya tabbatar wa manema labarai korar Alkali Aminu Kagara daga bakin aiki, kuma ya ce gwamnatin jihar tana nazarin hanyoyin da za ta bi domin taimaka wa makiyayan.
Barista Bawa ya shawarci jama’a su ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali, sannan su rika kai hankali nesa tare da tuntubar magabata game da duk wani sabani.